✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsadar gidan haya ta jefa iyalai cikin halin kaka-ni-ka yi a Legas

Ga dukkan alamu tsadar gidajen haya a sassa da dama na jihar Legas ya jefa mazauna jihar cikin halin kaka-ni-ka –yi har ta kai wasu…

Irin gidajen hayan da suke da tsada a LegasGa dukkan alamu tsadar gidajen haya a sassa da dama na jihar Legas ya jefa mazauna jihar cikin halin kaka-ni-ka –yi har ta kai wasu magidanta sun mayar da iyalansu jihohinsu na asali, wasu da suka yi sabon aure sun kasa tarewa da matansu wasu matasa kuwa sun kasa yin auren saboda fargabar samun gidan hayan da za su kama.
Binciken Aminiya ya gano cewa kafin a ba mutum hayar daki daya sai ya kashe Naira dubu dari, daki biyu na tafi-da-gidanka sai mutum ya kashe Naira dubu dari hudu zuwa dubu dari biyar, daki uku na tafi-da-gidanka wato filat sai mutum ya kashe Naira dubu dari takwas zuwa miliyan daya.
Kudin hayan ya bambanta daga unguwar zuwa unguwa. Wurare kamar unguwar Ikeja da cikin garin Legas da unguwar Lekki da bI da Ajah da kuma bakin taku da Surulere da Apapa suna da tsada sosai. Unguwanni kamar su Agege da Idi-Araba da Ogba da Oko-Oba da Mil 12 da kuma Ketu tsadar su ba ta kai na sauran ba. Sannan unguwanin kamar Alaba da Badagiri da Ikorodu ba su da tsada sosai amma duk da haka sai talaka ya yi da gaske kafin ya iya biyan kudin haya.
A jihar Legas masu gidan haya ba sa karbar kudin shekara guda sai shekara biyu zuwa sama tare da kudin yarjejeniya tsakanin maigida da dan haya da kudin wuta da na ruwa da na shara duk da dokar da gwamnatin jihar ta yi wacce ta ba dan haya ’yancin biyan kudin wata shida ko shakara daya.
Mutane da dama da Aminiya ta tattauna da su sun bayyana takaicinsu dangane da halin kunci da tsadar haya ta jefa su.
 Malam Abdul Wahab Usman ya ce ‘Gaskiya na shiga matsala sosai saboda ina zaune da iyalina a wani gidan haya sai aka sayar da gidan aka ce mu tashi. Ga shi a lokacin ba ni da kudin da zan kama daki. Dole na tura iyalina wani wuri kafin na sami daki. A yanzu sai ka tanadi kimanin dubu dari kafi a ba ka daki daya. Domin sai ka biya kudin shekara biyu da kudin yarjejeniya. Ka ga idan dakin ya kama Naira dubu 30 a shekara za ka biya dubu 60 tare da dubu 30 ta yarjejniya, za ka biya kudin wuta da na ruwa ga kudin shara da sauransu. Ka ga za ka kashe Naira dubu dari kenan ko ma fiye da haka. Idan kuwa dakin tafi- da- gidanka ne sai ka tanadi Naira dubu dari uku zuwa dubu dari hudu. Idan kuwa filat ne mai daki uku sai dai miliyan daya. To ina talaka zai iya samun wannan kudi’.
Shi kuwa Muhammadu Bello ya ce ‘Gaskiya ina zaune tare da iyalina sai aka tashe ni daga gidan da nake haya, dole na mayar da matata gidan iyayenta tare da dana. Saboda matsalar gidan haya da tsadar haya, yau shekara ta daya ba na zaune tare da iyalina. Gidan da aka tashe ni  wanda ya sayi gidan ya gaya min cewa shi Naira miliyan daya za a ba shi kudin haya. Mafiyawanci mutanenmu Hausawa su ne suke sa kudin haya ya yi tsada a Legas domin idan Bahaushe ya sayi gida burinsa ya sa ku cikin kunci mai makon su rika taimaka mana ba sa yi sai dai idan suka sayi gidan da kuke ciki sai dai su ba ku dubu ishirin-ishirin wai ku cika ku kama haya’.
Wani matashi mai suna Mustafa Musa Hadeja wanda ya kasa aure sakamakon tsadar gidan haya ya ce ‘Tsadar gidan haya ta jefa ni cikin matsala daban-daban. Ga shi yanazu ina son na yi aure amma saboda tsadar haya na ka sa yin aure. Domin idan talaka kamar ni ka ce za ka yi aure a lokaci guda kuma ka kama gidan da za ka zauna to gaskiya ba karamar matasala ba ce. Ni ba zan ce Hausawa ’yan’uwanmu ne suke da laifi gaba daya ba amma su ma suna da laifi. Mutum ne zai sayi gidan da mutum 50 suke zaune amma sai ya rushe ya mayar da shi gidan da mutum biyar za su zauna’.
Malam Adamu Musa wanda ya kasa tarewa da amaryarsa saboda tsadar gidan haya a Legas.
Ya ce ‘A lokacin da na yi aure na kasa tarewa da amaryata saboda tsadar haya dole sai gidansu na mayar da ita ni kuwa nake kwana a wani wuri daga bisani sai na mayar da ita garinmu na dawo na ci gaba da zaman ci-ranina.Dole kabilun yarabawan da muke zaune tare da su su rika yi mana wulakanci domin sai ka ga Bahaushe ya sayi gidan da mutum dari suke zaune ya rushe ya mayar da shi gidan da shi kadai zai zauna. Ka ga wannan ci baya ne’.
Wani magidanci da ya mallaki gidan haya mai suna Alhaji Umar ya musanta zargin da jama’a suka yi na dora alhakin kan Hausawa da masu gidan haya.
Ya ce ‘Matsalar mutanemu ita ce son banza. Sannan ba mu da hadin kai. Yaushe mutum zai sayi gida da tsada ka yi tunanin cewa zai ba ka ka zauna kyauta. Ai akwai wuraren da idan ka ji kudin hayar ma sai ka yi mamaki saboda yawan kudin. Ana taimakawa domin ni kaina akwai lokacin da wani Bayarabe ya zo ya nemi na bashi shagon da wani bahaushe yake haya cewa zai ba ni duk abinda nake so sai na ki saboda wanda yake ciki dan’uwana ne bahaushe’.
Wani katikan gida kuma mai nemawa mutane haya Mista Sunda Ajayi ya musanta zargin da aka yi musu na cewa suna da hannu wajen tsadar haya a Legas.
Ya ce, ‘Ba ma kara kudin haya masu gida ne suka karawa kuma suna yin haka ne saboda yadda abubuwan masarufi suka yi tsada. Sannan ga haraji da gwamnati take karba daga hannunsu’.
Gwamnatin jihar Legas ta yi doka cewa duk wani maigidan haya da aka kama ya karbi kudin fiye da shekara guda za a hukunta shi amma duk da haka ba ta canza zani ba. Domin idan ka ce wa maigida gwamnati ta yi doka kan kudin haya sai ya ki ba ka gida ko ma ya tashe ka daga gidansa.Wannan matsala ta sa mutane ba sa iya kalubalantar masu gidaje a Legas.