Da Dumi Dumi

Tsakanin Bukola Saraki da Bola Tinubu (2)

Dimokuradiyyar da ake tutiya da ita, ko’ina a duniya ba a maganar bambancin addini ko kabila ko bangare sai dokoki da ke kunshe a Kundin Tsarin Mulki. Koda Hassan da Hussain ne jama’a suka hadu, suka zaba a matsayin Shugaban kasa da Mataimaki shi ke nan, haka koda mahaifi ne da dansa, ko miji da matarsa.
Ba a maganar karba-karba ko ra’ayin wani tsohon soja. Da ma Musulunci adalci ya fi bai wa fifiko, komai da’awar mutum da Musulunci idan azzalumi ne Allah bai yarda a ba shi amana ba. Mulki yana dauwama ne da adalci, Allah (SWT) Yana barin mulki ya dade a hannun adali koda ba Musulmi ba ne, ya gaggauta kwace mulkin daga hannun azzalumi ko da Musulmi ne.
Babu wani addini da ya yarda da zalunci, sata, cin hanci, rashawa, kisa, tsafi, satar mutane, zina, luwadi da madigo. Kowanne akwai hukunci a kansa, mai tsanani ga duk wanda ya aikata ba tare da kowane irin bambanci ba. Amma su masu mulkinmu suke yi don ba a hukunta su. Shi ne babban aikin wannan gwamnati da wadanda suke tsoron haduwarsu da Allah, a hadu a kwato duk abin da kowa ya sata a hukunta masu kowane irin laifi kamar yadda Allah Ya yi umarni.
Daga Allah muke, ga Allah za mu koma. Ko ana so ko ba a so Musulunci abin da ya koyar shi ne, idan Allah Ya wadata mutum, kada ya bari makwabtansa na gidaje arba’in-arba’in Gabas da Yamma, Kudu da Arewa koda mutum daya ya kwana da yunwa idan ya sani, gwargadon wadatar da Allah Ya yi masa.
Duk shekara ya kasa dukiyarsa da ta shekara, kashi arba’in, ya bayar da kashi daya Zakka (1/40) ga matalauta masu tsananin bukata, wadanda ba sa cikin wadanda yake ciyarwa, kamar iyalansa. Amma su masu mulkin namu wadanda suka kamata a bai wa Zakka suke yi wa satar, su rabe tsakaninsu da wadansu sarakuna da malaman addini da abokansu masu yi musu kasuwanci da kudin da suka sace mana.
Babu maganar fitar da Zakka balle taimakon makwabta. Duk shugabannin da suka rabe rijiyoyin mai da sarakunan da suka sammar mawa, babu wani dan kasuwa cikinsu ko dan bangaren da ake hako man sai wadanda suke so ya wakilce su a bangaren da ake hako man suke tsarawa su zama gwamnoni, su yi ta tura musu makudan kudi suna rikewa, ba sa aikata wa talakawansu komai, shi ya sa ake samun tsageru a cikinsu suke sayar da rayuwarsu a kan yin  tu’annati ga gwamnati.   Cikakken misali shi ne James Ibori da Alamieyeseigha.
Idan ana so a magance wannan matsalar, sai an kwace duk rijiyoyin man da masu mulki suka mallakar wa kansu da sarakuna da ’yan korensu a kididdige duk kudaden da suka samu daga rijiyoyin man, su biya mu gaba daya.
Ba na neman kowace alfarma daga wurin kowa sai fafutikar nema wa kowa hakkinsa, a yi wa kowa adalci. Duk lalacewar duniya ba a rasa na Allah. Allah ma ba zai bar mu kacokan a hannun makiyansa, makiyan bayinsa, azzalumai, fajirai, matsafa ba. Shi ya sa ba ma saurara wa kowane irin azzalumi, har sai ya daina zalunci. Allah ma ba Ya yafe wa azzalumai zaluncin da suka yi wa bayinSa, sai idan bayin naSa ne suka yafe musu.
Babu wani abin tsoro ga kowane mutum, ballantana barawo, fajiri, azzalumi, Allah Shi ne kadai abin tsoro, Shi ne Mai rayawa, Mai kashewa, Mai arzurtawa, Mai talautawa, Mai bayar da mulki, Mai kwacewa. Allah ne kadai dauwamamme, kowa sai ya mutu babu wanda ya isa ya zabi lokacin da zai mutu, ko irin mutuwar ko wurin da zai mutu. Allah Ya sa mu cika da imani!
Alhaji Abdulkarim daiyabu shi ne Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya,  Tsohon Shugaban Jam’iyyar AD na kasa, Tsohon Shugaban kungiyar ’Yan Kasuwa da Masu Masana’antu da Ma’adanai da Harkokin Noma ta Jihar Kano (KACCIMA).
08060116666, 08023106666.