✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsarin gadon dabi’u da siffofin halitta (genetics) (7)

Matashiya Ga wadanda suke bibiyar wannan shafi a kullum, a yau mun waiwayo don ci gaba da silsilar da muka faro a shekarar da ta…

Matashiya

Ga wadanda suke bibiyar wannan shafi a kullum, a yau mun waiwayo don ci gaba da silsilar da muka faro a shekarar da ta gabata kan Tsarin Gadon dabi’u da Siffofin Halitta a kimiyyance, fannin ilmin kimiyya na musamman da a harshen Turancin zamani ake kira Genetics.  A makonnin baya, idan ba a manta ba, mun dakata ne a kashi na shida, inda mai karatu ya karanta bayanai kan gudunmawar fannin kimiyya da fasahar sadarwar zamani ga wannan fanni a duniyar yau.  Wato yadda masana harkar sadarwa da kwamfuta suka gina masarrafai ko manhajojin da suke taimakawa wajen tarawa, da tantancewa, da kuma taskance adadin dabi’un halittar dan Adam da ake ta aiki a kansa shekaru kusan 20 da suka gabata.  Idan ba a manta ba dai, a nan muka dakata.  A yau kuma za mu ci gaba.

Tsarin Jirkita dabi’un Halittar Irin Abinci
A yau za mu dubi wani bangare ne daga cikin bangarorin da wannan fanni mai fadi ke dauke da su.  Wannan bangare kuwa shi ne bangaren da ke lura da kokarin masana kimiyyar dabi’ar halittar halittu wajen sauyawa ko jirkita dabi’un halittar irin abinci da muke shukawa a gonakinmu, don samar da wasu nau’ukan iri na abinci masu dauke da yanayi da dabi’un da suka sha bamban da na asali.  Me ya sa malaman kimiyya ke yin haka?  Wadanne irin abinci ne aka jirkita asalin dabi’unsu?  Wadanne kasashe suka shahara da haka?  Meye alfanun da ke tattare da yin hakan a kimiyyance, da kuma fannin tattalin arzikin kasa?  Shin hakan na da wani cutarwa ne?  In eh, me da me ake tsoro?  Wannan bangare ne na musamman da ke fannin Tsarin Gadon dabi’u da Siffofin Halitta, kuma a Turance shi ake kira: Genetic Modification of Crops, ko GMC a gajarce.

Ma’ana da Asali
Kamar yadda bayani ya gabata a sama, wannan bangare da ake kira GMC shi ne yin amfani da kwarewar ilimin kimiyyar halittu wajen cirewa ko kara a kalla daya daga cikin kwayoyin dabi’un halitta (Genes) da ke cikin Tubalin Halittar (Cells) irin shuka na abinci (Crop Seed), don samar da wata fa’ida ta musamman.  Hanyar da ake amfani da ita wajen yin hakan kuwa ita ce hanyar Magance Tangardar dabi’un Halitta, wato Genetic Engineering. Wannan ita ce sabuwar hanyar aiwatar da wannan tsari.  Ta sha bamban da hanyoyin da manoman da ke amfani, kamar hanyar aure tsakanin nau’uka mabanbanta daga cikin dabbobi ko irin shuka, wadanda aka fi sani da: Selectibe Breeding, da Somaclonal bariation.
Wannan sabon fanni ya samo asali ne daga kasar Amurka sama da shekaru ashirin da suka gabata.  An fara sayar da nau’ukan jirkitattun irin abinci a kasar ne cikin shekarar 1994.  Kafin wannan lokaci, masana sun fara gano wannan dabara ne tun cikin shekarar 1946, cewa ana iya daukar dabi’ar halittar wani irin shuki, a sanya wa wani.  Cikin shekarar 1988 aka samu shukin farko ta wannan sabuwar hanya. Wannan nau’in shuka kuwa shi ne na sabon nau’in shukar taba mai iya jure kwayoyin bateriya da ke kashe shuke-shuken abinci.
Ana shiga shekarar 1994 kuma sai ga sabon nau’in irin shuka na tumatur, jirkitacce, mai iya jure tsawon lokaci bayan an tsinko daga gona, ba tare da ya zama tubus ba balle ya zagwanye.  Wannan nau’in sabon iri bai jure tsawon lokaci ba saboda dan Karen tsada da kamfanin ya tsawwala masa.  A shekarar 1995 kuma sai ga sabon irin masara jirkitacce, da waken soya, da kuma tumatur dai har wa yau.  Ana shiga shekarar 2000 sai aka samar da nau’in shinkafa da suka kira Golden Rice, wanda aka jirkita shi don magance matsalolin ciwon ido ta hanyar shigar sinadaran bitamin A a cikinsa. Zuwa shekarar 2011 an tabbatar da cewa kasar Amurka ce a gaba wajen samar da ire-iren wadannan jirkitattun nau’ukan irin shuka na abinci.  An kiyasta cewa akwai a kalla nau’ukan irin shuka guda 25 jirkitattu a kasar, kuma kashi 91 cikin 100 na waken soya da ke kasar duk jirkitaccen iri ne, kashi 81 na masarar kasar jirkitaciya ce, haka kashi 88 cikin 100 na irin audugar kasar shi ma duk jirkitacce ne.
Tsarin Jirkitawa
Wannan sabon tsarin inganta irin shuka, kamar yadda masu goyon bayan tsarin suke cewa, yana aukuwa ne ta hanyar debo daya daga cikin dabi’’un halittar wata irin shuka, a sa shi cikin Madarar dabi’ar Halitta (DNA) na irin shukan da ake son jirkitawa, don wata fa’ida ta musamman. Misali, masana kan iya daukar wani nau’in irin shuka na masarar wata kasa a Afirka, irin wanda ke jure zafin rana, da jure rashin noma na tsawon lokaci, sai a dauki daya daga cikin nau’in dabi’un halitta (Genes) da ke cikin wannan irin masara na Afirka, a shigar cikin Madarar dabi’ar Halittar (DNA) masarar kasar Amurka da ba ya iya jure zafin rana ko rashin noma na tsawon lokaci.  Da zarar an shigar da wannan kwayar halitta, sai a ci gaba da renon wannan irin kwayar shuka da aka masa kari a dakin binciken kimiyya (Science Laboratory); daga tsira har girbewa.  
A kasar Amurka misali, kamfanonin samar da amfanin gona ne ke tafiyar da wannan tsari. Kamfani zai nemi izini wajen hukuma don yin gwaji. Da zarar hukuma ta ba su damar gwaji sai kama gwaji.  Idan kamfani ya gama gwajin nau’in irin shukan da ya samar, babu matsala, sai ya sake neman izini wajen hukuma kan nomawa tare da sayar da wannan nau’in irin shuka da ya samar a gonarsa.  A halin yanzu akwai kamfanoni sama da uku a kasar Amurka masu tafiyar da wannan aiki; a wajensu kadai ake iya sayan irin shuka jirkitattu.
Muhawara Tsakanin Masana
Tun sadda wannan tsari na jirkita dabi’un halittar irin shuka ya bayyana, babu shekarar da za ta shiga har ta kare ba tare da samun muhawara mai zafi a tsakanin masana kimiyyar halittu da dabbobi ba.  Wannan muhawara kuwa kan kankama ne tsakanin masu goyon bayan wannan tsari, don tabbatar da inganci ko alfanunsa, da kuma wadanda ke ganin tsari ne mummuna da nan gaba zai kawo cikas a rayuwar duniya baki dayanta, ba ma kasar Amurka ba.  Wannan muhawara ne ya raba kasashen duniya masu arzikin tattali zuwa biyu.  kasar Amurka na bangaren masu goyon bayan wannan tsari, domin kashi 90 cikin 100 na nau’ukan abincin da ake sayarwa a shagunan abincin kasar Amurka duk daga jirkitattun nau’in irin shuka aka samar da su.  A daya bangaren kuma akwai kasashen Nahiyar Turai da ke ganin wannan tsarin bincike ne mai hadari da bai kamata a danganta shi ga abincin mutane da dabbobi ba.  

(Za mu ci gaba)

Wasu daga cikin sakonninku

Assalaamu Alaikum Baban Sadik, na ji bayananka a kan ‘yan Dandatsa, Allah kara basira, amin.  Tambaya ta ita ce: wai idan an sace bayanai daga kwamfuta, mai ita zai iya dawowa da bayanan?  In zai iya, ta yaya? Kuma masu Dandatsanci ba su ne idan an kama su ake kashe su ba?  – Daga Sani S.S. Indabawa
Wa alaikumus salaam, Malam Sani barka da warhaka.  Dangane da bayanan da aka sace daga kwamfuta, ya danganci tsarin da barawon yayi amfani da su.  Su bayanai a cikin kwamfuta a tsarin siginar lantarki suke, wato Digital Form. Idan kwamfutar a kunne take, dan Dandatsa na iya shiga daga wata Uwa duniya muddin a jone take da Intanet, ya sace abin da yake son sacewa na bayanai, ya canza abin da yake son canzawa na tsare-tsaren kwamfutar (kamar sunan mai kwamfutar, da kalmomin da yake amfani dasu wajen shiganta), ba tare da mai kwamfutar ya sani ba.  Amma duk da sace su da yayi, wannan bai hana idan ka bude kwamfutarka ka gansu, sai in goge su ya yi bayan sacewa.  Domin su bayanan kamar yadda na fada da farko, a tsarin siginar lantarki suke; kwafansu kawai ake yi a barsu.  Mutum biliyan na iya kwafansu ba tare da sun kare ba.  Amma idan bayan ya kwafi bayanan sai kuma ya goge su (wato: Delete) to a nan kuma babu yadda za a yi ka mallake su.  Ko kuma bayan ya sace, sai ya kulle su ta amfani da kwarewarsa na ilimi kwamfuta, to a nan kuma sai dai ka ta hakilon neman wanda zai warware maka dabarun da ya yi amfani da su wajen aiwatar da wannan danyen aiki nashi.
Su ’Yan Dandatsa ‘yan ta’adda ne, masu amfani da kwarewarsa wajen satan bayanai ko kona su, ko tara su a matsayin shara ga wata kwamfutar da manufar haddasa mata illa.  Babu isassun dokoki a kasashen duniya kan hukuncin da ya kamata a musu, in ka kebe kasashen da suka ci gaba.  Ko a can din ma, galibi sai dai a kulle su na tsawon watanni ko shekaru tare da tara mai tsanani, ko kuma a hana su amfani da kwamfuta idan kananan yara ne da ba su kai shekaru 18 ba.  Amma har yanzu ban taba jin wani dan Dandatsa da aka kashe ba sanadiyyar abin da ya gudanar na aikin dandantsanci.  Da fatan ka gamsu.