✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsarin Ma’adanar Bayanai a Kimiyyance (5)

Matashiya A makon jiya mun fara bayani kan asali da samuwar fasahar faifan DBD, wato: “Digital Bersatile Disc,” da dalilan da suka sa kamfanonin sadarwa da…

Matashiya

A makon jiya mun fara bayani kan asali da samuwar fasahar faifan DBD, wato: “Digital Bersatile Disc,” da dalilan da suka sa kamfanonin sadarwa da kere-keren kayayyakin lantarki irin su Toshiba da Sony da Philips suka samar, ta hadin gwiwa da kamfanonin kwamfuta irin su IBM da Apple da Microsoft da sauran makamantansu. A wannan mako in Allah Ya yarda za mu yi tsokaci ne kan tsari da na’ukan fasahar faifan DBD.

Tsari da Kintsin Fasahar Faifan DBD

Cikin 1995 dai aka tabbatar da kundin fasahar faifan DBD, bayan daidaituwar da aka samu a tsakanin kamfanonin lantarki, kamar yadda bayani ya gabata a makon jiya.  Wannan sabuwar fasaha ta zo da nau’o’in sauye-sauye masu armashi idan aka kwatanta ta da wacce ta gabace ta a wancan lokaci na baya. Kundin da ke dauke da daukacin siffofi da tsarin fasahar faifan DBD, wato: “DBD Book,” ya tsara yadda faifai zai kasance.

Da farko dai fasahar faifan DBD na dauke ne da mizanin ma’adana mai girman 4.7GB, wato za a iya zuba bayanai sama da tiriliyan hudu da digo bakwai ke nan. Sannan wannan faifai ya kasu kashi biyu. Akwai mai falle daya, wato: “Single Layer DBD” ke nan. Sai kuma mai dauke da tagwayen falle, wato: “Dual Layer DBD.”  Wannan nau’i na biyu yana dauke da mafi girman mizani. Mafi karancin mizaninsa shi ne wanda ke iya daukar bayanai tiriliyan takwas da digo biyar, wato: 8.5GB.

Faifan DBD dai, kamar faifan CD da bayaninsa ya gabata a makonnin baya, an kera shi ne daga gasasshiyar roba. Kuma an yi amfani da injin bula roba ne don dabba’a wadannan faya-fayai da dimbin yawa cikin kankanin lokaci. Wannan inji ana kiransa: “Injection Moulding Machine.”  Wannan inji yana dauke ne da wata allura mai karfin gaske, wadda ke huda roba kowane iri ne.  Sai kuma wasu hannaye na musamman, wadanda ke lailaya roba bayan injin ya huda ta.

Nau’o’in Fasahar Faifan DBD

Kamar yadda bayani ya gabata a sama, akwai manyan nau’o’i biyu dangane da siffa ko madauki da faifan DBD ya zo da su. Ta bangaren nau’in bayanan da Faifan DBD zai iya dauka kuma, akwai nau’o’i da dama; wasu masu dauke da fallen faifai daya (Single Layer) ne, wasu kuma masu dauke da tagwayen fallen faifai (Dual Layer).  Kowanne daga cikin wadannan nau’o’i yana da kundin da ke dauke da bayanin tsari da kintsinsa a kimiyyance.

Akwai nau’in Faifan DBD mai daukar sauti zalla. Wannan shi ake kira: DBD-Audio. Ire-iren wadannan nau’o’i suna zuwa ne dauke da wakoki, kuma idan ka saya, sai dai ka dora su kan na’urar sarrafa DBD, wato: “DBD Player” don sauraron wakokin, ko a kwamfuta mai dauke da na’urar sarrafa DBD, wato: DBD+R. Sai nau’i na biyu mai suna: DBD-Bideo. Wannan nau’in shi kuma yana zuwa ne da bayanan bidiyo zalla, musamman daga kamfanonin fina-finai na duniya, irin su: “Warner Bros” da sauransu.  Wadanna nau’o’i biyu ba a iya goge abin da ke cikinsu, muddin aka taskance bayanan da ke ciki tun daga kamfanin da ya kera su.

Kashi na uku kuma shi ne nau’in DBD-ROM, wanda ke zuwa galibi dauke da babbar manhajar kwamfuta (ko na kamfanin Microsoft ko Apple). Ko wasu nau’o’in manhajojin kwamfuta.  Abin da kalma ko haruffan “ROM” ke nufi shi ne: “Read Only Memroy.”  Shi ma idan aka saya, ba a iya goge bayanan da ke ciki ko kadan, sun zauna ke nan daram – zuwan sojan Badakkare. Kashi na hudu shi ne: DBD-R, wato: “Recordable” ke nan.  Galibi irin wannan nau’in DBD kan zo ne holokonsa; babu komai a ciki. Ana saya ne don zuba bayanai a ciki da nufin taskance su kadai, ko taskance su da kuma saurare ko kallo idan nau’in hoto ne ko bidiyo ko kuma hotuna. Su ma da zarar ka taskance bayanan da ke cikinsu, to, ba ka iya goge su, ko kadan.

Sai kashi na biyar, wanda ake kira: DBD-RW, wato: “Rewritable” ke nan.  Abin da wannan kalma ke nufi shi ne, kana iya goge bayanan da ka zuba a ciki, sannan ka sake zubawa ko taskance wasu. Shi ma wannan nau’in DBD ana sayensa ne holoko; babu komai a ciki. Idan ka saya, sai ka zuba bayanan da kake bukata. In ka ga dama kuma ka goge su kai-tsaye. Sai kashi shida da ake kira: DBD-RAM, wato: “Random Access Memory.”  Wannan nau’i na DBD kuma ana amfani da shi ne a kwamfuta kadai. Faifai ne na DBD wanda ke matsayin ma’adanar wucin-gadi, wato: “RAM” ke nan. Idan aka dora wa kwamfuta, ba a cirewa sai an kashe, misali. Shi ma ba a iya goge bayanan da ke cikinsa.

Bayan wadannan, akwai wadanda suka kebanci kwamfuta ne zalla. Wadannan su ne masu tagwayen faifai, wadanda mizaninsu mafi karanci shi ne tiriliyan takwas da digo biyar (8.5GB). Daga ciki akwai nau’in DBD+R, wanda shi kuma yakan zo ne da bayanai a cikinsa, amma kuma a kwamfuta kadai ake iya sarrafa su. Kuma ba a iya goge abin da ke ciki, saboda a kulle suke. Kusan iri daya da nau’in DBD-R ke nan, bambancinsu kawai shi ne, shi DBD-R kan zo holoko ne, babu komai a ciki. Sai kuma nau’in DBD+RW, wanda shi kuma ke zuwa da bayanai a ciki amma a kwamfuta ake iya sarrafa su. Wadannan nau’uka dai masu dauke da tagwayen faifai ne, wato: “Dual Layer DBD.”  Suna amfani ne da wani tsari mai suna: “Opposite Track Path,” wajen sarrafa bayanan sauti ko bidiyo da suke dauke da shi. Idan faifan farko ya kare, nan take sai wannan tsari na OTP ya yi farat ya tsallaka zuwa titin da ke dauke da faifan bayanai na biyu, don ci gaba.