✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon dan kwallon Super Eagles Thompson Oliha ya mutu

Thompson Oliha, tsohon dan wasan kulab din Super Eagles kuma daya daga cikin ’yan wasan da suka yi nasarar lashe gasar cin kofin Nahiyar Afirka…

Thompson Oliha, tsohon dan wasan kulab din Super Eagles kuma daya daga cikin ’yan wasan da suka yi nasarar lashe gasar cin kofin Nahiyar Afirka da aka gudanar a kasar Tunisiya a shekarar 1994 ya mutu a lokacin da yake shekara 45 a duniya.
Thompson Oliha ya mutu ne a ranar Lahadin ta da gabata a wani asibiti mai zaman kansa da ake kira Yusjib Industrial Medicare da ke garin Ilorin a Jihar Kwara bayan da ya fadi a bayan gidansa.
Daga bisani an kai shi babban asibitin garin inda shugaban asibitin mai suna Dokta Abdulraheem Yusuf ya tabbatar da mutuwar sa ga manema labarai.
Kafin mutuwarsa Oliha ya rika yin amai babu kakkautawa jim kadan bayan ya jagoranci kungiyar kwallon kafa ta Kwara Football Academy  inda ta lallasa kulob din Ben Mackezie na kasar Mali a ranar Asabar din da ta gabata a filin wasa na garin Ilorin.
Abokin aikinsa da ke lura da kananan ’yan wasan kwallon kafa na Kwara Academy, Paul Odey ya yi alnihinin mutuwar Oliha inda ya ce tuni aka ajiye gawarsa a dakin ajiyar gawarwaki na asibitin Ilorin bayan an sanar da iyalansa.
Oliha da aka haifa a birnin Benin da ke jihar Edo a ranar daya ga watan Oktoban 1968 ya bugawa kungiyoyin kwallon kafa da dama a kasashen Afirka da na Turai.
Ya bugawa kulob din Bendal Insurance da kulob din Iwanyanwu Nationale  daga shekarar 1985 zuwa shekarar 1991.
Sannan ya yi wasa a kulob din Africa Sport a shekarar 1992 da kuma kulob din Maccabi Ironi Ashdod FC a shekarar 1993 zuwa 1994 da kuma kulob din Antalyaspor daga shekarar 1994 zuwa 1995.
Ya yi ritaya yana da shekara 27 da haihuwa sakamakon raunin da ya samu a gwiwa.
Kafin ya yi ritaya Oliha ya buga wa kulab din Super Eagles wasa sau 31 inda ya ci kwallaye biyu.
Ya fara buga wasansa a matsayin dan wasan kasa da kasa a shekarar 1990 a lokacin da kulob din Super Eagles ya yi wasan sada zumunci da kasar Senegal  sannan ya yi fitowarsa ta karshe a wasan da Najeriya ta yi da kasar Italiya a gasar cin kofin duniya  a shekarar 1994.