✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon jarumin Indiya Amita Bachchan ya ceto manoma 1,398 daga kangin bashi

Fitaccen jarumin fina-finan kasar Indiya Amita Bachchan, ya bayyana cewa ya biya wa wasu manoma bashin da ya kai fiye da dala dubu 500. Jarumin…

Fitaccen jarumin fina-finan kasar Indiya Amita Bachchan, ya bayyana cewa ya biya wa wasu manoma bashin da ya kai fiye da dala dubu 500.

Jarumin ya bayyana hakan ne a shafinsa na yanar gizo a ranar Talata, inda ya ce manoman da ya biyawa bashin sun kai 1,398.

Kuma dukkaninsu sun fito ne daga Jihar Uttar Pradesh, inda nan ne mahaifar Amitan.

Dubban manoma a kasar Indiya dai na fama da dumbin bashi, wanda sukan jima ba su biya ba.

Bangaren aikin noma na matukar samun koma baya a kasar, inda a wasu lokutan ba a fiye samun amfanin gona mai yawa ba.

An kiyasta cewa tun daga shekarar 1995, manoma akalla dubu 300 sun kashe kansu a kasar ta Indiya, saboda dalilin da ke da alaka da bashin da ake binsu kamar yadda BBC ta rairayo kididdigar.

Yawanci dai manoman na ciwo bashin ne daga bankuna kasar domin su yi aikin noma, to amma wajen biya ne ake kai ruwa rana.

Shi dai Amita yana daya daga cikin manyan jaruman kasar Indiya da suka yi suna a duniya. Sannan kuma jarumi ne da ya taba shiga harkar siyasa a baya.

An haife shi a ranar 11 ga watan Oktoban 1942, shekararsa 76 ke nan a duniya bana.

Ya fito a fina-finai fiye da 190, kazalika ya fito a fina-finan da ba na kasarsa ba, wato fina-finan Hollywood.

Ya kan gabatar da manyan shirye-shirye a gidan talbijin din kasarsa wadanda mutane ke son kalla, bama a kasar ba kawai ba, har ma da wasu kasashen duniya.

Ya auri jaruma Jaya Bachchan, inda suka haifi ’ya’ya biyu mace da namiji, namijin Abhishek Bachchan, shi ma jarumi ne, kuma ya auri jaruma Aishwarya Rai.