✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Turkiyya ta mayar da martani bayan harin sojin Syria

Kasar Turkiyya ta ce ta kai harin ramuwar gayya ne bayan da sojojin  Syria sun kai harin da ya hallaka mata sojinta akalla shida tare…

Kasar Turkiyya ta ce ta kai harin ramuwar gayya ne bayan da sojojin  Syria sun kai harin da ya hallaka mata sojinta akalla shida tare da wani farar hula guda, wanda ke aiki da rundunar sojin Turkiyyar a yankin nan na Idlib da yaki ya daidaita.

Ministan tsaron Turkiyyar, ya fada a yau Litinin cewa hare-haren sojin saman Syria sun jikkata sojin Turkiyyar bakwai a wani yanki da ya rage a hannun ‘yan tawaye inda suka yi tunga a kasar ta Syria.

Wannan lamarin na iya kara zafafa zaman tankiya tsakanin gwamnatocin Turkiyyar da kuma Syria, sakamakon yadda ba a cika samun fada gaba da gaba tsakaninsu ba a baya. Hakan zai kuma iya haifar da tsamin dangantaka tsakanin mahukuntan biranen Moscow da kuma Ankara, wadanda dukkaninsu suka nemi samar da daidaito a yakin da suke yi a Syria.

Da yake magana da manema labarai kafin ya tashi zuwa Ukraine, Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyyar ya bayyana cewa, martanin da suka mayar din ya kunshi harin da jiragen yaki da kuma manyan bindigogin atilari kan wasu muradun kasar Syria.

Erdogan, din ya ce martanin ya kashe tsakanin mayaka 30 zuwa 35 na Syria.