✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Waƙoƙin Makaɗa

A ci gaba da kawo muku nazari a kan fagen fasaha da Aminiya ke yi a wannan mako mun zo kawo muku waƙokin makada da…

A ci gaba da kawo muku nazari a kan fagen fasaha da Aminiya ke yi a wannan mako mun zo kawo muku waƙokin makada da wadansu daga cikin mawaka suka yi lokacin da suke rera waka. Kiɗa da waƙa wasu abubuwa ne biyu da suke da dangantaka ta ƙut-da-ƙut da juna. Bayan haka sun daɗe suna ɗaukar hankalin al’ummar Hausawa wajen rarrabewa. Amma duk da wannan kusanci da kiɗa da waƙa suke da shi, suna da bambanci. A wasu halayen akan samu mutane suna rera waƙa ba tare da kiɗa ba, haka ma akan rangaɗa kiɗa ba tare da waƙa ba. Sai dai an fi yin waƙa ba tare da kiɗa ba:

 

Kiɗa

Zarruƙ, Kafin Hausa da Al-Hassan (1987), sun wassafa kiɗa a matsayin: “Wanzar da daddaɗan amo daga abubuwan bugawa, ko na gogawa ko na busawa ko kuma na girgizawa.”

A wurare kamar na kai amarya ko lokutan aikin gona ko lokacin aikin mata a cikin gida da ɗaukar gara da gaɗa da mata kan yi da lokutan tatsuniya sa lokutan wasan yara da sauransu, akan rera waƙa ba tare da kiɗa ba. Haka kuma a wurare kamar mahauta lokacin da aka yanka dabbar da girmanta ba saban ba, akan daɗe ana rangada kiɗan kalangu ba tare da waƙa ba, sai kuma samari da kan yi ’yan bushe-bushensu ta hanyar amfani da bambaro ko sharewa ko sarewa ko liƙo da sauransu ba tare da waƙa ba, kawai don nishaɗi kamar yadda zai zo nan gaba.

 

Waƙa

Yahaya, Zariya, Gusau, da ’Yar’aduwa (1992), sun ce, “Waƙa zance ne sarrafaffe, aunanne wanda ake aiwatar da shi ta bin hawa da saukar murya, mai zuwa a gunduwoyin layuka da ake rerawa bisa wani daidaitaccen tsari.”

Ke nan, idan aka lura da waɗannan ma’anoni guda biyu, za mu ga kowane ɗaya daga cikinsu zaman kansa yake yi wato kiɗa daban, haka nan ma waƙa. Sai dai, a manne suke, wato tare ake yin su ke nan.

Amma sau da yawa, idan aka ambaci kiɗa, ko aka ce makaɗi, ko kaɗe-kaɗe, abin da ke zuwa tunanin Bahaushe da farko shi ne kiɗa da waƙa. Wannan kuma haka abin yake a fagen nazari da kuma mu’amalar yau-da-kullum. Dubi maganar Junaidu da ’Yar’aduwa (2002), inda suka ce, “Makaɗa, su ne mutanen da suka rungumi kiɗa da waƙa suka zama hanyar gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.” Haka idan muka leƙa maganar Farfesa Ɗangambo (1984), inda yake cewa, “Waƙoƙim makaɗa, sun kasu zuwa kashi-kashi…”

Abin lura a nan shi ne zuwan kalmar kiɗa tare da waƙa a cikin waɗancan maganganu guda biyu na masana da suka gabata na ƙarfafa maganar da ta gabace su. Saboda haka, a wannan rubutu an yi amfani da waɗannan kalmomi biyu a matsayin abu guda. Musamman wajen karkasa su mawaƙan.

 

Rabe-Raben Makaɗa

Farfesa Ɗangambo (1984), ya bayyana cewa abin lura wajen rarraba mawaƙa ko makaɗa shi ne nau’in waƙoƙi, jigon waƙoƙi, kaɗe-kaɗe, dalilan yin waƙa da kuma irin nau’in mutanen da aka rera wa waƙar.

Kusan ma idan aka lura da rabe-raben da masana suka kawo a rubuce-rubucensu, za a fahimci cewa sun fi karkata ne ga rukuni ko nau’in mutanen da ake yi wa waƙar. Daga cikin irin waɗannan masana akwai, Farfesa Ɗangambo (1984), Junaidu da ’Yar’aduwa (2002), Yahaya, Zariya, Gusau, da ’Yar’aduwa (1992), sai kuma Zarruƙ, Kafin Hausa da Al-Hassan (1987).

 

Sun kawo rabe-raben kiɗa ko makaɗa kamar haka:

1.           Makaɗan Fada.

2.           Makaɗan Sarauta.

3.           Makaɗan Jama’a.

4.           Makaɗan Maza.

5.           Makaɗan Mata.

6.           Makaɗan Ban-Dariya.

7.           Makaɗan Sana’a.

Amfanin Kiɗa

Kiɗa da waƙa na da matuƙar tasiri a rayuwar Bahaushe. Al’ada ce mai ƙarfi. Wani abu ne da ya shafi rayuwar Bahaushe baƙi ɗayanta. Kai a bisa gaskiya ma, idan muka leƙa karan-kataf ɗin al’adun Bahaushe, babu wacce ba kiɗa da waƙa a cikinta in ban da mutuwa. Misali, fara daga kan aure, suna, sana’a, bukukuwa, zaman nishaɗi, yaƙi da sauransu, za mu ga cewa duk ana yi musu kiɗa da waƙa ciki kuma har da malamai. Saboda haka cikin kiɗa da waƙa akan samu abubuwa kamar:

1 Nishaɗantarwa: Nishaɗi shi ne ƙashin-bayan waƙa. A kan yi waƙa don a faranta wa wanda ake yi wa waƙar ya ji daɗi, ya kuma bayar da kyauta. Farfesa Ɗangambo (1984), ya ce, “Wannan aji na ban-dariya, babban aji ne, domin kuwa ya ƙunshi duk wasu kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe waɗanda suka ƙunshi raha, nishaɗi da ban-dariya.”

2 Ƙarfafa Gwiwa: Daga cikin amfanin kiɗa da waƙa akwai ƙarfafa gwiwa. Misali, idan muka ɗauki rukunin makaɗan maza, sukan yi kiɗansu ne don zaburantar da gwarzon da suke yi wa waƙa, su zuga shi ya ƙara dagewa wajen fafatawa da abokin wasansa kamar a ce wasan dambe ko kokawa da makamantansu. Dubi yadda Ɗan’anace ya ke zuga Duna inda yake cewa, “…Ba a wa mutum takakka, Wandara kai ɗai ke wa mutum takakka, in ka so ka ko buge shi ka dawo…”

3 Ilimantarwa: Akwai ilimantarwa a cikin kiɗa da waƙa. Ta hanyar kiɗa da waƙa akan koyi azancin magana, karin magana, iya sarrafa harshe, a wasu lokutan ma da sanin tarihi. Misali, idan aka ɗauki waƙar Musa Ɗanƙwairo ta Sarkin Daura wacce a cikinta ya bayyana asalin Hausa Bakwai a tarihance. Haka in aka lura da waƙar Ɗanmaraya Jos ta Duniya Budurwar Wawa yadda yake ilimantar da mai sauraro game da duniya.

4 Samar da aikin yi: Waƙa sana’a ce. Saboda haka tana samar da ayyukan yi ga masu yin ta.

5 Adana tarihi da al’adu: Ta hanyar waƙa ana iya fahimtar yadda al’adun Hausawa suke da kuma tirihinsu.

Mun ciro wani sashi na wannan rubutu daga: Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano da kuma shafin rumbun ilimi na In.