✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wadanda cutar Cobid-19 ta hallaka sun haura 2000

A farkon makon nan, jami’an kiwon lafiya a China, suka tabbatar da cewa, adadin mutanen da suka kamu da cutar Coronabirus (Cobid-19), ya zarce dubu 70,…

A farkon makon nan, jami’an kiwon lafiya a China, suka tabbatar da cewa, adadin mutanen da suka kamu da cutar Coronabirus (Cobid-19), ya zarce dubu 70, yayin da wadanda suka rasu ya haura mutum 2000. Sai dai kimanin mutum dubu 11 da suka kamu da cutar sun warke.

Hukumomi a Lardin Hubei na kasar China, inda cutar ta samo asali, sun ce a farkon makon nan, an samu karin mutum 100 da suka mutu sanadiyyar cutar, yayin da karin wadansu ma’aikatan lafiya suka isa yankin, don taimaka wa fannin kiwon lafiya da ya shiga wani hali bayan barkewar cutar a watan Disamban bara.

An tabo batun wannan babbar barazana da cutar Cobid-19 ke yi wa duniya, a wani babban taron na tsaro na duniya da aka yi a birnin Munich na kasar Jamus, inda Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi tsokaci.

Ya ce, “Duniya na kashe biliyoyin daloli wajen tunkarar hare-haren ta’addanci, amma ba a a kyakkyawan shiri kan barkewar wata cuta, wanda hakan hadari ne da zai shafi rayuka da tattalin arziki da siyasa da al’amuran yau da kullum.”

 

…Ta haifar da karuwar bukatar shatar jiragen sama

Kasuwar masu shatar jiragen sama na ci gaba da bunkasa, sakamakon karuwar bukatar shatar jiragen daga fasinjoji da ke bukatar zirga-zirga a daidai lokacin da cutar Cobid-19 ke yaduwa.

Yayin da jiragen sama ke rage zirga-zirga zuwa ko fita daga China, wadansu matafiya sun rasa na yi a ciki da wajen kasar. Attijarai  daga cikinsu na amfani da dukiyarsu wajen shatar kananan jiragen sama na alfarma domin daukarsu, duk da tsadar hakan.

Sai dai kamfanonin na kin amsar tayin haka daga gare su, bisa dalilin haramta zirga-zirga a China ko ma rashin jiragen a kasa da ma matukansu.

Wani kamfanin Singapore mai suna MyJet Asia, ya ce ya samu karuwar bukatar hayar jiragensa da kashi 80 -90 cikin 100 a watan jiya kawai. “Mutane da dama sun fita daga kasar China lokacin bikin Sabuwar Shekarar Kasar, kuma yanzu sun zaku su ga sun koma cikin kasarsu,” injji Logan Rabishkansar, Babban Jami’in Kamfanin MyJet Asia. Da dama sun bukaci a mayar da su biranen Beijing da Shanghai da kuma Hong Kong.

Karamin jirgi na daukar tsakanin fasinja biyu zuwa hudu, a kan Dalar Amurka 2,400 (kimanin Naira dubu 864) a kowace sa’a, ya danganta da girman harkar da za a yi. Matsakaici kuwa na daukar mutum takwas zuwa 10  a kan Dala 6000 (kimanin Naira miliyan 2 da dubu 160) a kowace sa’a.

Hakazalika wani kamfanin mai suna BistaJet ya ce ya samu gagarumar karuwar bukatar jiragensa domin shatarsu a  watan jiya, duk da cewa ya dakatar da zirga zirgar shiga da fita a China.

Sababbin masu kamuwa da cutar sun ragu

Hukumomin lafiya a kasar China sun ce alkaluma 1,886 na sababbin masu kamuwa da kwayar cutar Cobid-19 aka samu wanda ya  zama adadi mafi karanci da aka samu a rana guda a wannan wata. Sababbin alkaluman sun nuna an samu karin mutum 98 da suka rasu a Lardin Hubei.

Hukumomin sun ce raguwar alkaluman wata alama ce da ke nuna matakan da ake dauka na shawo kan cutar na yin tasiri.

A Talatar had ta gabata, ukumomin lafiya a China sun ce suna aiki don samar da sababbin allurai da magungunan cutar da hanyoyin tantace jinin mara lafiya da kuma kare rayuwar likitoci.

A waje guda kuma hukumomin lafiya a Japan sun ce za su fara gwajin amfani da maganin cutar kanjamau don warkar da marasa lafiya da suka kamu da cutar Cobid-19.

An kebe dan kasar China a Kenya saboda Cobid-19

An kebe wani dan kasar China da ke aiki a wani kamfanin gina hanya a Arewa maso Gabashin Nairobi babban birnin kasar Kenya, a wani mataki na gudun yaduwar cutar Cobid-19.

Babu wata alama da ta nuna mutumin wanda ke aiki a kamfanin kasarsu a Kenya yana dauke da cutar. An dai kebe shi ne a Mutomo da ke yankin Kitui, kuma ana mika masa abinci ne ta taga, in ji jaridar Daily Nation.

Kamfanin dai ya aike da wata wasika ga mahukuntan yankin a kan cewa an kebe musu ma’aikaci bayan isowarsa kasar daga Lardin Hubei da ke Arewa maso Gabashin China.