✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Waiwaye kan darussan baya (7)

A wannan mukala ta  Tuna Baya…. mun kwana a karkashin bayanin mu’amala da masu karatu, amma saboda mu ji dadin gudanar karatun, za mu fara…

Dan barandan ‘Facebook’, dauke da sanhonsa na bayanaiA wannan mukala ta  Tuna Baya…. mun kwana a karkashin bayanin mu’amala da masu karatu, amma saboda mu ji dadin gudanar karatun, za mu fara daga farkonsa, kamar haka:
Mu’amala da Masu Karatu
A wannan zango ma kamar sauran zangunan da suka gabata, masu karatu sun rubuto tambayoyi, wasu na amsa su nan take, wasu kuma na buga su, wasu kuma, wadanda maimaitattu ne, ban saurare su ba.  Sannan akwai wadanda suka bugo waya don nuna gamsuwa, ko don godiya ko kuma neman karin bayani kan kasidar da suka karanta a makon, nakan saurare su, duk da cewa na ce ba a kira, sai dai a rubuto tes.  dan Adam ajizi ne.  Akwai kuma wadanda suka rubuto don bukatar kasidun baya, su ma nakan aika musu.  Wasu in aika musu nan take, wasu kuma sai bayan wani lokaci. Ya dai danganci halin da na samu kaina sadda suka aiko bukatarsu.
Har wa yau a cikin wannan zango na samu sakonnin gyara sosai daga wajen masu karatu.  Shahararre daga cikinsu shi ne wanda na samu daga Malam Auwal Yakubu, wani masanin fannin kimiyyar sararin samaniya.  Na kuma buga a wannan shafi, ina kuma mika godiyata a gare shi matuka. Allah saka masa da alheri.  
Akwai wadanda suka aiko mini da sakonni kan wani abin da suka ga na rubuta wanda bai musu daidai ba, ba don cewa abin da na fada ne bai yi daidai ba; nakan musu karin bayani, kuma sukan ce kada a buga a shafin jarida, kuma ban buga ba.  A iya zatona, da wanda ya min gyara ya ce a buga don jama’a su gani (tunda a baya sun ga kuskurena), da wanda ya ce kada a buga, a dai gyara, duk na dauka sun yi hakan ne don Allah, don kuma neman gyara, kuma Allah Ya saka musu da alheri baki daya.
Bayan haka, akwai wadanda ke daukar lambar wayar da suka gani a shafin, su yi ta min filashin.  Idan na kira sai a ce kawai a jarida aka gani.  To, na dai sha bayani kan ladubban kiran waya, da kuma cewa idan ba ka da kudi a wayarka da zai wadatar da ka kira, ka yi tes, in babu na tes, ka hakura ko ka je inda ake buga waya na kudi ka kira.  Hakan ya fi mutunci. Yin filashin idan ba ga wanda ya sanka ya kuma san lambarka ba, kuskure ne matuka, sai in ya zama tsananin lalura.  Don Allah mu kiyaye.
Bayan haka, na san masu karatu sun ga canjin yanayi a wannan shafi, ma’ana wasu lokuta akan ji ni shiru, babu abin karatu a shafin.  Wannan ya faru ne sanadiyyar kalubalen rayuwa da na yi ta cin karo da su a wannan zango.  Ba korafi nake ba, sai don bayani.  Wannan kalubale ne ya yi tasiri matuka kan rayuwata, ciki har da rubutun da nake yi a wannan shafi.  Don haka a gafarce ni, in Allah Ya yarda al’amura za su daidaita nan kusa.  Wannan ne ma ya sa na ce kasidun wannan zango ba su kammala ba, ma’ana akwai wadanda idan aka bukace su daga gare ni ba za a same su ba.  Wannan ya faru ne sanadiyyar rasa kwamfuta ta da na yi, kamar yadda bayani ya gabata a baya.  Amma wani abin farin ciki kuma shi ne, duk kasidar da aka bukata a wajena ba a samu ba, za a samu a shafin Mudawwanarmu da ke: http://fasahar-intanet.blogspot.com, da kuma http://kimiyyah.blogspot.com. Sai a garzaya.
Kammalawa
A karshe dai, ina mika godiyata ga dukkan masu karatu; tsakanin masu bugo waya da masu rubuto tes da wadanda ma ba a jin duriyarsu, wanda su ne suka fi yawa.  Allah saka wa kowa da alheri.  Ina mika godiyata ga Editan Aminiya Malam Bello Muhammad Zaki da irin gudunmawar da yake ba ni, tare da hakuri da ni sanadiyyar halin da na samu kaina.  Sai godiya ga Malam Abubakar AbdurRahman Dodo da Malam Ahmad Garba, masu lura da wannan shafi nawa. Ina godiya gare su matuka, musamman wajen shawarwari da suke ba ni kan yadda zan inganta  shafin baki daya.  Sannan ina godiya ga kamfanin Media Trust, tare da mika ta’aziyyata ga hukumar kamfanin kan rasuwar Manajin Edita, Malam Suleiman Muhammad.  Allah gafarta masa, Ya sa Aljanna ce makomarsa, Ya kuma kyautata namu karshen.  Hakika na san Malam Suleiman sosai tun shekarar 1998, yana cikin mutanen da suka yi tasiri matuka a rayuwata kan harkar rubutu.  Allah gafarta masa.  
Sannan kuma shafin Kimiyya da kere-kere na mika godiyarsa ga Sashen Hausa na BBC da irin sanayyar da suke baiwa shafin wajen gayyata na ofishinsu da yin hira da ni kan al’amuran da ke faruwa a fannonin kimiyyar sadarwa musamman, da kuma amsa tambayoyin masu sauraronsu.  Su ma a wannan zango sun gayyace ni kusan sau goma zuwa ofishinsu da ke nan Abuja. Ina godiya matuka, musamman ga Babban Edita, Malam Bashir Sa’ad Abdullahi, da sauran ma’aikatansu irin su: Ibrahim Mijinyawa da Raliya Zubairu da Naziru Minka’ilu da sauransu.  
Jama’a, zan dakata a nan, sai Allah Ya hada mu a mako mai zuwa.