✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasan takalmin taya ya fara bunkasa a garin Kaduna -Abubakar Super Coach

Shugaban kungiyar wasan takalmin taya na Jihar Kaduna Malam Abubakar Super Coach ya ce wasan takalmin taya ya fara kankama a Jihar Kaduna da ma…

Abubakar Super Coach, Shugaban Kungiyar masu wasa da takalmin tayaShugaban kungiyar wasan takalmin taya na Jihar Kaduna Malam Abubakar Super Coach ya ce wasan takalmin taya ya fara kankama a Jihar Kaduna da ma a Jihohin Arewa.
Shugaban ya ce suna gudanar da wasannin tayar ne don nishadantar da al’umma a kowane lungu da kuma sako da ke Jihar Kaduna da ma a kasa baki daya.
Ya ce kungiyar tana bunkasa ne ganin yadda a kullum take samun yawan matasan da ke shiga don a dama da su.  Ya ce a yanzu haka kungiyar tana da membobin da suka yi rajista da ita da suka kai kusan 200 da suka fito daga sassa daban-daban a garin Kaduna.
Ya ce babban burin kungiyar shi ne ta karade fadin kasar nan a wasannin takalmin taya.
Ya ce wasan takalmin taya yana hada kan matasa walau ma’aikata da ’yan kasuwa da masu zaman kashe wando kuma hakan na taimakawa wajen dauke hankalin matasa daga aikata miyagun dabi’u musamman masu zaman kashe wando.
Ya ce babban ofishinsu yana harabar dandalin Murtala ne da ke Kaduna inda ya hori matasa su yi amfani da wannan dama don ganin sun yi rajista don su koyi yadda ake wasa da takalmin taya.
Ya ce mata ma ba a bar su a baya ba, don haka akwai matasa maza da mata da yanzu haka suka kware a harkar wasan takalmin taya da ko’ina suka shiga za su burge walau a gida ko a kasashen ketare.
Daga nan sai ya yi kira ga gwamnati ta tallafa musu da rance don ba su damar sayo kayayyakin wasanni don raba su ga matasan da suke son shiga kungiyar amma ba su da halin sayen takalman saboda tsada. Ya ce burin kungiyar shi ne ta wakilci Najeriya a gasar wasanni ta Olamfik a bangaren gudun takalmin taya a wasannin Olamfik da za a yi nan gaba.