✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasu ’yan bindiga sun kashe wani Tela a Kaduna

Wasu ’yan bindiga sun kashe wani tela a gidansa da ke Unguwar Kabala a yankin karamar Hukumar Kaduna ta Kudu da ke jihar Kaduna.Rahotonni daga…

Wasu ’yan bindiga sun kashe wani tela a gidansa da ke Unguwar Kabala a yankin karamar Hukumar Kaduna ta Kudu da ke jihar Kaduna.
Rahotonni daga yankin sun bayyana cewa ’yan bindigan sun isa gidan Alhaji Surajo Sani Tela ne da misalin karfe 12:00 daren litinin kuma suka bukaci ya ba su kudi bayan ya ba su ne suka  fito da shi waje suka harbeshi sannan suka saka shi cikin bayan  motarsa suka rufe.
A cewar wani makwabcinsa wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce: “Da safe da muka samu labarin abun da ya faru kanmu ya daure sosai. Saboda ba mu san abun da ya yi masu ba domin shi dai tela ne kawai sai dai wasu lokuta yakan yi tafiye-tafiye zuwa sayo yaduka a kasashen waje. Babu wanda yasan dalilin da ya sa aka kashi shi da kuma ko su waye suka aikata hakan,” inji shi.
Amma wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa zaton ’yan fashi ne domin sun maharani sun bukaci mai dakin mamacin da ta ba su gwalagwalai kuma sun karbi kudi wajensa kafin suka halaka shi.
’Yan daba sun kashe wani matashi
A wata sabuwa kuma wani matashi ya rasa ransa bayan sararsa da wasu suka yi a unguwar Hayin Malam Bello da ke Kaduna.
Wannan al’amari ya faru ne da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Litinin. Aminiya ta ziyarci kofar gidan sarkin Hayin Malam Bello, inda ta tarar da ’yan sanda a tsaitsaye cikin shirin ko ta kwana.
A cewar daya daga cikin ’yan sandan mamacin da aka kashe yana daga cikin matasan da suka yi rikici a ’yan kwanakin baya a garin Rigasa.
“Kwannan nan matasa ’yan sara suka yi fada a Rigasa inda mutum uku suka rasa ransu. Muna ganin daga cikin yan daban ne suka biyo wannan suka kashe shi a wani shiri na ramuwar gayya. Ka ga ke nan bamu gama binciken wancen kisan ba gashi sun sake kashe wani,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa: “Matsalar da jami’an  tsaro ke fuskanta a kokarinsu na kawo karshen aikin ’yan daba a garin  shi ne da zarar sun kama irin wadannan matasa sai iyayensu, a wasu lokutan ma har da wasu masu unguwanni, sai ka ga  suna sintirin zuwa ofishin ’yan sanda suna neman a sakar masu ’ya’ya.”
Kodayake, wakilinmu ya tuntubi jami’an Hulda da jama’a na rundunar ’Yan sandan Jihar, SP Aminu Lawan ta wayar tarho amma bai amsa wayarsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.