✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata mata ta sake kashe mijinta da wuka a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wata matar aure mai shekara 19, mai suna, Rabi Shamsudden a kauyen Danjanku Tasha a Karamar Hukumar Malumfashi…

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wata matar aure mai shekara 19, mai suna, Rabi Shamsudden a kauyen Danjanku Tasha a Karamar Hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.

An kama matar ne ana tuhumarta da kashe mijinta mai suna Shamsudden Salisu ta hanyar soka masa wuka, wanda hakan ya yi ajalinsa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Gambo Isah, ne ya tabbatar da hakan inda ya ce, Rabi ta kashe mijinta ne ta hanyar amfani da wuka da misalin karfe 4:00 na asubahin yau Litinin.

Gambo, ya kara da cewa makwabtan gidan su Rabi sun ji lokaci da marigayin ke neman taimakon jama’a. Da isar makwabtan cikin gaggawa gidan sun tarar an kulle gidan, su suka yanke shawarar haurawa ta katangar gidan.