✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wutar lantarki ta hallaki wani ma’aikaci a Kalaba

Wayar wutar lantarki ta yi sanadiyyar mutuwar wani ma’aikacin kamfanin rarraba wutar lantarki a Kalaba, inda yana cikin aiki gyara wutar lantarkin sai aka mai…

Wayar wutar lantarki ta yi sanadiyyar mutuwar wani ma’aikacin kamfanin rarraba wutar lantarki a Kalaba, inda yana cikin aiki gyara wutar lantarkin sai aka mai do da wutar.                                                                                                   Wannan al’amari ya faru ne a harabar Jami’ar Kalaba a makon jiya.

Bayanin da wakilinmu ya samu ya ce, mamacin mai suna Micheal Enang Edu yana aiki ne da Kamfanin Lantarki (EDC) da ke jihar.

Wani wanda hadarin ya faru yana kusa da wurin mai suna Edet Ekpenyong, ya shaida wa Aminiya cewa marigayi Micheal Edu ya gamu da ajalinsa ne yayin  da yake kokarin hada wata wayar wutar lantarki da ta katse alhali shi da wadansu abokan aikinsa ba su dade da gama aikin yanke wutar ba, da masu amfani da ita ba su biya ba. Bayan sun tafi ne sai shi kuma ya hau kan turken wutar yana kokarin mayar da wayar sai aka dawo da wutar, inda nan take wutar ta kama shi ya makale a jikin turken.

Wakilinmu ya tuntubi Dokta Joe Ekpang, Jami’in Watsa Labarai na Jami’ar Kalaba domin jin ta bakinsa game da matsalar. Ya ce tabbas al’amarin ya faru.

Marigayi Micheal Enang, ya fito ne daga kauyen Antani-Adadama da ke karamar Hukumar Abu, Jihar Kuros Riba.