Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Ya bukaci a kafa manyan kasuwanni a iyakokin kasa

An yi kira ga Gwamnatin Tarraya ta kafa manyan kasuwanni a garuruwan da suke kan iyakokin kasar nan domin habaka tattalin arzikin kasa da kuma sauran kasashen Afirka da ke da iyaka da ita.

Wani fitaccen dan siyasa a Jihar Kebbi Alhaji Sahabi Lolo ne ya yi wannan kira a lokacin da yake zantawa da Aminiya a garin Lolo inda Nigeriya ta yi iyaka da Jamhuriyyar Benin da kuma Jamhuriyar Nijar.

ADVERTISEMENT

Alhaji Sahabi ya fadi haka, saboda alkawarin da Gwamnatin Jihar Kebbi ta yi tun shekarar 2014 na kafa kasuwar duniya da tashar aje kaya da ake shigowa da su daga kasashen ketare da kuma fita da su zuwa waje.

Ya ce garin Lolo yana da duk abubuwan da ake bukata na kafa wannan kasuwar duniya da za ta samar da kayayyakin da suka shafi shinkafa da kifi da shanu, kuma akwai hanyoyin shigowa da kaya daga waje ta Kogin Kwara da hanyar kasa inda kowane mako ’yan kasuwa suke zuwa daga kasashen Mali da Senegal da Nijar da Jamhuriyar Benin.

ADVERTISEMENT

A karshe Lolo ya yi godiya ga Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu bisa kokarin da yake yi na ganin wannan alkawari ya cika don kara dankon zumunci a tsakanin Najeriya da sauran kasashen Afirka.