Search
Subscribe
Ya dace jami’an Kwastam su riKa bin motocin da suka dauko shinkafa a tsakanin jihohi suna kamawa?

Ya dace jami’an Kwastam su riKa bin motocin da suka dauko shinkafa a tsakanin jihohi suna kamawa?

Bayan da Gwamnatin Tarayya ta hana shigo da shinkafa cikin Kasar nan, a baya-bayan nan ma’aikatan Hukumar Kwastam sun shiga bin motoci a tsakanin jihohi da suke zargin suna dauke da shinkafa ba tare da tantance yaya aka yi shinkafar ta shigo Kasar nan daga Kasashen ketare ba. Da zarar dan kasuwa ya sayo shinkafar daga wani gari domin zuwa ya sayar a shagonsa a garinsu, sai jami’an Kwastam su tare, wai ya shigo da kayan da gwamnati ta haramta shigo da shi. Irin wannan dabi’a ta jami’an Kwastam  akasarin lokuta kan haifar da haddura wani lokacin har da asarar rai. Kuma hakan ya sa wakilanmu suka jiyo ra’ayoyin jama’a kan dacewa da rashin dacewar haka:

 

A gaskiya bai da ce ba – Alhaji Abubakar Ambursa

Daga Adam Umar, Abuja

A gaskiya bai dace ba saboda yana shafar wadanda ba su ji ba ba su gani ba. Kamata ya yi su Karfafa matakan tsaro a kan iyaka. Ba daidai ba ne a riKa bari har sai an shigo da kaya zuwa gari, ko kuma an karbi wani abu daga kan iyaka, sannan daga baya a bi su zuwa kan hanya ko shago ko gida ana Kwace kaya ba. Hakan zai Kara talauta jama’a ne kawai da kuma raba su da sana’a.

 

Zalunci ne kawai–Na-Mashaya

Daga Bashir Lawal Zakka, Birnin Kebbi

A nawa ra’ayin bai dace jami”an Kwastam su riKa bin motocin da suka dauko shinkafa ba, saboda zai iya sa a yi sanadin rasa rayukan jama’a da dukiyoyinsu. Kuma me ya sa suka bari har aka shigo da shinkafar, tun daga kan iyakar Kasa, don haka yin hakan ya zama zalunci ke nan.

 

Bai dace su riKa bin motocin ba – Abdullahi Skate

Daga Kabir Yayo Ali, Ibadan

Bai dace jami’an Kwastam su riKa bin motoci dauke da buhunan shinkafa a kan hanyoyi da kasuwannin cikin gida ba, domin duk kayan Kasasashen Ketare da ka gani a cikin gida sun shigo ne ta kan iyakokin Kasa, inda aka girke jami’an Kwastam domin hana shigo da kayan. Kuma bayan jami’an Kwastam, akwai wadansu jami’an tsaro daban da suka kafa shingen bincike da dukkansu suka kasa yin aikinsu. Kuma shinkafar da ake nomawa a Najeriya ba za ta ishe mu ba. Kamata ya yi gwamnati ta Kyale a riKa shigo da shinkafa kadan daga Ketare da za su yi tafiya tare da shinkafar cikin gida har zuwa nan gaba da shinkafar gida za ta mamaye komai.

 

Bai dace ba ko kadan– Ustaz Tahir Zubairu

Daga Kabir Yayo Ali, Ibadan

Kamata ya yi jami’an Kwastam su dauki tsauraran matakan daKile fasa Kwaurin shigo da shinkafa a kan iyakokin Kasa da sauran hanyoyin boye. Wannan ne babban aikin da ya rataya a wuyansu wajen gyaran Kasa. Muddin aka yi amfani da wannan mataki zai Karfafa wa manoma gwiwa wajen noma shinkafar da za ta wadaci Kasa. Amma bai dace ba ko kadan jami’an Kwastam su riKa kama irin wannan kaya a kan hanyoyi bayan an riga an Ketaro da su cikin Kasa. Sai idan mun nuna kishin Kasar haihuwarmu ne za mu kai ga nasara.

 

Ya kamata su hana shigowa da kayan tun daga kan iyaka– Malam Misbahu Isa

Daga Adam Umar, Abuja

A gaskiya bai dace ba kuma ai babu abin da zai Kari gwamnati. Ya kamata su tabbatar da hana shigowa da kayan tun daga kan iyaka. Idan ma’aikata ne ba su wadatar ba, ga zaratan matasa da ke neman aiki a dauke su. Idan kuwa kayan aikin ne babu, to a saya musu. Amma shigowarsu har cikin gari suna kama kaya bala’i ne, bai kuma dace ba, don yana jawo a samu asarar rayukan al’umma a irin wannan bin da suke yi wa motocin da suka dauko shinkafar.

 

Ya yi daidai –Yusuf Mustapha Batsari

Daga Bashir Lawal Zakka, Birnin Kebbi

Ni a nawa ra’ayin jami’an Kwastam da suke bin motocin dauko shinkafa ya yi daidai. Saboda gwamnati ta sa dokar hana shigo da shinkafa, a halin gaskiya ya dace saboda sun karya dokar kasa, domin dole dan Kasa ya bi dokar Kasa idan yana son ya zauna lafiya. Duk abin da ka ga gwamnati ta hana shi ga ’yan Kasa to yana da amfani ga al’ummar Kasarta, saboda haka jami’an Kwastam ba su da laifi ko kadan. Sai dai wadansu jami’an Kwastam din suna wuce gona da iri ba su bin dokar da gwamnati ta ba su.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin