✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya dace Majalisar Dokoki ta tsige Shugaba Jonathan – Isyaku Ibrahim

daya daga cikin dattawan da suka kafa Jam’iyyar PDP mai mulkin kasar nan Alhaji Isyaku Ibrahim ya ce ya kamata Majalisar Dokoki ta kasa ta…

daya daga cikin dattawan da suka kafa Jam’iyyar PDP mai mulkin kasar nan Alhaji Isyaku Ibrahim ya ce ya kamata Majalisar Dokoki ta kasa ta tsige Shugaba Goodluck Jonathan daga mulki.
Alhaji Isyaku Ibrahim ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Abuja, inda y ace Shugaba Jonathan ya aikata laifuffukan da suka isa a tsige shi daga mulki.
“Na daya shi ne batan-dabon da Dala biliyan 20 a kamfanin Man Fetur na kasa, na biyu shi ne rawar da ya rika yi a gangamin PDP na Kano bayan kwana daya da fashewar bam a Nyanya, Abuja, sai na uku sace fiye da ’yan mata 200 a garin Chibok na Jihar Borno a ranar da PDP ta yi gangamin na Kano,” inji shi.
Alhaji Isyaku Ibrahim wanda tsohon dan rusasshiyar Jam’iyyar NPN ne a Jamhuriya ya ce wani abin kaico da gwamnatin Jonathan ke yi shi ne yadda ake hayar ’yan ba-ni-na-iya suna fadin maganganu game da Gwamna Murtala Nyako wanda ya fadi gaskiya game da halin tsaron da ke addabar Arewa, musamman soki-burutsun da wani tsoho Mista Edwin Clark yake ta yi cewa a kori gwamnonin jihohin Borno da Yobe da Adamawa a maye gurbinsu da sojoji.
 Ya kuma yi tir da yadda ake zargin Hukumar tsaro ta SSS da neman yin kazafi ga tsohon Gwamnan mulkin soja na Jihar Kaduna Kanar Abubakar dangiwa Umar domin tozarta shi, saboda ya bukaci a yi bincike kan kashe mazauna wani gidan da ba a kammala ba da jami’an tsaro suka yi a unguwar Apo da ke Abuja.
Alhaji Isyaku Ibrahim ya ce yadda jami’an tsaro suke mazurai yayin aikinsu, ba wanda zai iya ba su rahoton asiri. Don a da ana girmama kowa amma ba irin kama-karya na ’yan bana bakwai ba.
Yace dalilin da ya sa ya bar Jam’iyyar PDP, shi ne don ta kasa yin abin kwarai, sannan Shugaba Jonathan ya samu mulki ne a banza, shi ya sa yake ta harigido.