✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya gurfanar da amaryarsa a kotua kan kudin sadaki

Wani ango a Karamar Hukumar Kiyawa mai suna Bala Ali Kiyawa ya kai amaryarsa kotu a kan kudinta da ta biya masa sadaki. Kuma kotu…

Wani ango a Karamar Hukumar Kiyawa mai suna Bala Ali Kiyawa ya kai amaryarsa kotu a kan kudinta da ta biya masa sadaki. Kuma kotu ta umarci angon ya biya ta kudinta da ta ranta masa, Naira dubu 60 a matsayin sadaki da kudin kayan aure.

Ango Bala Aliyu wanda shi ne ya yi karar amaryar tasa da kansa, bayan ya sake ta, saboda yadda take bin sa wuraren sana’arsa tana tayar masa da hankali, ya gabatar da korafinsa a gaban kotun ne domin a yi musu iyaka.

Da yake yi wa alkali bayani, Bala ya ce ya saki matarsa bayan kwana 19 da daura masu aure bisa sabanin da ya shiga tsakaninsu. Ya ce, to, amma maimakon ta koma gidansu, sai ta ci gaba da zama a gidan da ya kama mata haya tana tara maza. Saboda haka ya gabatar da ita a gaban kotu domin kada ta jawo masa magana a nan gaba.

Ya ce matar tasa mai suna Rahama Bala da ke unguwar Mambila ita ce ta ranta masa kudi ya aure ta, saboda haka ya kawo kararta don ya san matsayin wancan kudin da take tunda dai ita Rahama ce ta bukaci ya sake ta.

Da take mayar da martani a gaban kotun, Malama Rahama cewa ta yi ita ce ta ranta masa kudin kuma hakkinta ne ya biya ta, ta ce abin da ya sa take tsayawa da wadansu maza, saboda ta gama idda a cikin kwana 45, kuma washegarin da ya sake ta ta yi jinin farko, haka zalika ita ’yar kasuwa ce, don haka ba ya da ikon hana ta tsayawa da maza domin aikinta saye da sayarwa.

Bayan sauraron dukan bangarorin ne Alkalin Kotun Shariar Musulunci da ke Kiyawa, Malam Muktari Shu’aibu Birnin Kudu ya yanke wa Bala Aliyu hukuncin ya biya Rahama kudinta cikin wata shida, duk wata zai rika biyanta Naira dubu daya.