Da Dumi Dumi

Ya kamata mata su zauna lafiya da mazansu – Hafsatu Yusuf

Hajiya Hafsatu Yusuf, tsohuwar Ma’aikaciyar Jinya ce, wadda a halin yanzu ta kafa gidauniya mai suna Gidauniyar Mothers of The Earth International Foundation. A hirarta da Aminiya ta bayyana ayyukan jinkan da take gabatarwa a karkashin kungiyar da sauran lamuran da suka shafi tarihinta:

 

Tarihina

Sunana Hajiya Hafsatu Yusuf, an haife ni a Maiduguri ranar 4 ga Oktoban 1968. Na fara karatu a makarantar firamare ta ’Ya’yan Sojoji (Army Children School) ta Maiduguri. Bayan na kammala sakandare sai na fara aiki a matsayin Ma’aikaciyar Jinya, wato Nas. Daga baya sai na bari na koma makaranta inda na yi karatun Malanta mai Daraja ta Daya (NCE). Bayan na kammala sai na wuce jami’a na yi digiri fannin ilimi.

ADVERTISEMENT

Aiki:

Kamar yadda na fada a baya na fara aikin asibiti ne a Maiduguri daga nan sai na yi aure. Ganin cewa mijina ba ya son ina barin gida ina zuwa aiki asibiti ko wani aiki daban sai na koma makaranta inda na yi NCE daga bisani kuma na wuce jami’a na yi karatun digiri.

 

Nasarori:

Na samu nasarori da dama a rayuwa, amma babbar nasarar da na samu ita ce ta kafa wannan gidauniya ta Mothers of the Earth International Foundation inda a kullum nake taimaka wa mutanen da suke neman taimako, musamman matan da mazansu suka rasu suka bar su da ’ya’ya. Don haka a gare ni babbar nasara ce yadda Allah Ya ba ni damar yin bakin kokarina wajen tallafa wa wanda yake cikin wani hali na neman taimako.

 

Ayyukan da nake gudanarwa a wannan gidauniya

Ina tallafa wa mata matasa da kuma wadanda mazansu suka rasu, wajen koya masu ayyukan hannu irin su dinki da saka tare da tallafa musu da jari da kuma kayan aiki don ganin sun dogara da kawunansu kuma sun tallafa wa yaransu don su je makaranta.

Sannan muna wayar da kawunansu a kan wasu abubuwa da suka shafi rayuwarsu. Misali muna wayar musu da kai a kan matsalar nan ta safarar mata da kananan yara zuwa kasashen waje da sunan za a sama musu aiki, inda a karshe suke fadawa cikin kunci, wato ko a sayar da su a matsayin bayi ko a sanya su cikin karuwanci ko su kasance cikin wani mummunan hali na da-na-sani.

Ka san akwai dimbin jama’a da matsalarsu ba ta wuce kawai su samu wanda zai tsaya ya yi musu magana cikin fara’a da jin dadi ba sannan ya ba su shawara. Don haka a duk lokacin da na ga na sanya wani mutum da yake cikin damuwa ya yi ko da murmushi ne to ni kuwa burina ya cika.

 

Kalubale

Akwai kalubale da dama, kada ka manta na yi aure ina karamar yarinya wanda hakan ya sanya na hada karatu da rainon iyali, don haka abin bai zo da sauki ba.

Sannan kalubalen da muke samu a wannan gidauniya, shi ne na rashin samun tallafi daga gwamnati ko masu hannu da shuni ko wasu kungiyoyi na ciki da wajen kasar nan. Har yanzu ba ma samun wani taimako daga waje. Da za mu samu wannan tallafi za mu ribanya irin ayyukan jinkan da muke yi a yanzu.

Sannan mukan ziyarci sansanonin ’yan gudun hijira na cikin gida da rikici ko  fadace-fadacen kabilanci suka daidaita. Kuma muna ba mata da yara irin wadannan horo na sana’o’in hannu sannan mu tallafa musu da kayan aiki da jari.

 

Bambancin rayuwa a yanzu da  lokacin da muke tasowa

A gaskiya ina tuna irin yadda na taso cikin ’yan uwa da abokan arziki, ga yayye ga kanne ga kawunai da sauran dangi duk inda na juya, nakan yi murna. Domin na fito daga babban gida ne.

A wancan lokacin abin yana da ban sha’awa. Lokacin duniya tana kwance, lafiya, rayuwa tana da sauki kwarai. Za ka ga makwabtaka an dauke ta da muhimmanci, za ka ga an zama kamar ’yan uwan juna. Sannan akwai tsaro za ka iya barin gida ka je makaranta komai dare ka dawo ba tare da wata fargaba ba. A gaskiya wancan lokaci rayuwa tana da sauki sosai. Don haka ya dace mu ci gaba da zama lafiya da juna  .

 

Burina a lokacin da nake matashiya

A lokacin da nake matashiya kamar yadda na fada mun taso cikin gata ga iyaye da sauran dangi, don haka muna cikin walwala. Kuma haka muke tsammanin rayuwa za ta ci gaba da tafiya, amma da na yi aure sai na gane ashe abin ba haka yake ba. Amma dai burina ina karama shi ne in ga na cimma burina a kan duk wani abu da na sanya a gaba.

 

Yadda na fara tunanin kafa wannan gidauniya ta Mothers of Earth International Foudation

To wannan suna da na sanya wa wannan gidauniya ya samo asali ne, da farko saboda mijina matukin jirgin sama ne. Duk da yake ba a hadarin jirgi ya rasu ba, amma akwai wasu abokan aikinsa da suka rasu a hadarin jirgi.

Wata rana na je ta’aziyyar daya daga cikin abokansa da ya rasu a wani hadarin jirgi, ina cikin falon gidansa sai na ga hotonsa tare da mamacin kafe a jikin bango. Da matarsa ta ga ina kallo sai ta je ta kirawo surukarta wato mahaifiyar mamacin ta fada mata cewa ta zo ta gaisa da matar wanda yake tare da mamacin a hoton wato ta nuna nuna wa surukar mijina a hoton.

Ita kuma surukar sai ta zo ta rungume ni, sannan ta kalli hoton ta fada da harshen Ingilshi “Oh mother earth only you could habe taken my child from me” wato ta nuna irin yadda mutuwa ce kawai za ta iya zuwa ta raba ta da danta farat daya kamar haka. Wannan magana tata ta ba ni tausayi. Ganin cewa matar nan da a ce za ta ga mutuwar a fili ma da sai inda karfinta ya kare kafin ta dauki danta.

Don haka koda na fara tunanin yadda zan kafa gidauniyar da zan rika tallafa wa matan da mazansu suka riga mu gidan gaskiya da na zo wajen zaben sunan da zan sanya mata sai wannan magana ta fado mini a rai. Wannan shi ne dalilin da ya sa na sanya mata wannan suna Mothers of The Earth International Foundation.

 

Yadda na hadu da mijina

Mun hadu ne a gidan makwabcinmu. Makwabcinmu kawunsa ne, ya zo daga ne Legas don ya ziyarce shi. Ni kuma ’ya’yan makwabcin namu kawayena ne. A lokacin an yi sa’a mun shigo gidan mu uku da ni da kawayen nawa biyu, shi kuma sun fito daga masallacin da ke gidan sai ya gan mu muna wucewa. Take sai ya nuna wa kawunsa ni, sannan ya fada masa cewa yana sona. Ka ji yadda abin ya fara.

 

Wane hali kika fi so game da mijinki?

Ina son halinsa na kafewa a kan duk wani abu da ya san shi ne daidai. Sannan ina matukar son yadda yake kirana da sunana. Shi yana kirana da Misis Yusuf ne. Akwai lokacin da wani makwabcinmu ya tambaye shi, “Shin me ya sa kake kiran matarka da sunanta?” Sai ya fada masa cewa “Saboda ita abokiyata ce, kuma matata ce.”

 

Yara

Muna da ’ya’ya uku, maza biyu sai mace daya.

 

Yadda nake ji a matsayina na uwa

A gaskiya farin cikin ba zai misaltu ba. A gare ni ina ganin haihuwa wata babbar baiwa ce daga Allah. Zan iya tunawa sa’ar da na fara daukar dan da na haifa jim kadan bayan haihuwarsa, farin cikin ba zai misaltu ba, ina kallon ina rike da wata babbar baiwa ce da Allah Ya ba ni.

 

Wuraren da na ziyarta suka baki sha’awa

Na taba zuwa (dajin) Yankari (a Jihar Bauchi). Kuma ina sa ran wata rana zan sake komawa. A lokacin da na je ban dade da yin aure ba, kai ina tunanin shi ne wuri na farko da muka fara ziyarta bayan na yi aure. Ban mantawa a lokacin bisa kuskure sai na ajiye wani abu a bakin kofa, ai kuwa sai wani biri ya zo ya dauka, sai na fara fadin “Ah, ya dauke mini….”

Don haka a gaskiya ina sha’awar komawa. Ina jin ana maganar Obudu ma yana da kyau, kuma ina sa ran wata rana zan je can. Na taba zuwa wasu wurare biyu a wajen kasar nan, amma dai babu kamar gida

 

Yadda nake yin hutu

Idan na tashi daga aiki, sai in je gida in duba sakonnin waya da aka turo mini kuma in mayar da amsa ga wasu sakonnin na email sannan in karanta jarida. Ban cika damuwa da kallon talabijin ko sauraren rediyo ba. Na fi son in zauna wurin da ba surutu kamar minti 20 zuwa 30 ya wadatar.

 

Abincin da na fi so

Dari bisa dari na fi son in ci tuwo da miyar kuka, ban da mu ba ko da zan ci shi sau uku a rana.

 

Wakar da na fi so?

Ina son jin kidan gurmi ko kuma Jazz

 

Shawarar da mahaifiyata ta taba ba ni da ba zan manta ba

Ina tunawa a kullum idan zan fita takan ce da ni, , “Ki kama kanki.”

 

 Shawarata ga mata da matasa

Ina ba su shawara su kama kansu kuma su zauna lafiya da mazansu da iyalansu da kuma sauran mutane, sannan su kama sana’a.

Sannan kuma su kula da iyalansu su rika taimaka musu tare da yin hakuri da juna. Sannan su kasance uwaye ga kowa. Domin da a ce mata za su dauki wadannan matakan da duk wani kalubale da ake da shi yanzu a cikin al’umma ya kau.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya