Da Dumi Dumi

Yadda ake burodin ayaba

Barkanmu da sake saduwa da ku a wannan filin namu na girke-girke. Tare da fatar ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwadawa domin karya kumallo ko don yi wa wadanda aka gayyato cin abinci. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu ci gaba da kawo muku nau’o’in girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata

• Flawa

• Kwai

• Sukari

ADVERTISEMENT

• ‘baking powder’

• Ayaba

• Madara

• Bata

Hadi

A samu ayaba guda biyu a kwaba su da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sai a zuba ‘baking powder’ da sukari da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sai a fasa kwai biyu da wannan kwababbiyar ayaba a cikin fulawar da aka yi mata hadi da sukari da sauransu. Sai a gauraya su sosai su kwabu. Sannan a dauko tukunyar gasa burodi a zuba sai a saka a gidan gasa burodi. Bayan minti 45, sai a cire.

Za a iya cin wannan hadin burodi da shayi a lokacin karin kummallo. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandani sabon salon burodi.

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya