✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake hada kek din wake

Kayan hadi Wake Sukari Bakar hoda Kwai Bota Yadda ake yi:- Da farko uwargida za ki sami wake mai kyau sai ki bayar a barza…

Kayan hadi

  • Wake
  • Sukari
  • Bakar hoda
  • Kwai
  • Bota

Yadda ake yi:-

Da farko uwargida za ki sami wake mai kyau sai ki bayar a barza miki shi a inji. Idan aka kawo sai ki bakace domin duk bawo da bakin da ke jikin waken ya fita. idan ki ka tabbatar ya gyaru sosai sai ki bayar akai miki inji a nika shi ya yi laushi sosai. Sanann sia ki tankade.

Sai ki ajiye shi a gefe daya. Sannan ki samo mazubin da za ki kwaba kek din a ciki sai ki zuba sukari da bota ki juya su sosai, sanan ki kawo kwai ki fasa akai ki ci gaba da juyawa idan kika tabbatar ya biyu. (anan wasu suna amfani da injin na mider wanda hanya ce da take da sauki da kuma kyau wajen kwabin kek) sannan sai ki dauko garin wakenki ki zuba tare da bakar hoda akan wancan kwabin sai ki ci gaba da juyawa

kamar yadda ake yi wa fulawa. Idan kika gama sai ki dauko mazubin kek din ki shafa masa man bota  ajiki sannan ki zuzzzuba kullun a ciki.

Sannan sai ki jera su a abin da kike yin gashi da shi. Ki barshi tsawon mintuna 20. Idan ya gasu za ki ji yana kanshi.