✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda APC da PDP suka sa zare kan Dokar Zabe

Jam’iyya mai mulki ta APC da babbar jam’iyyar hamayya ta PDP sun sa kafar wando daya kan sabuwar Dokar Zabe da zauruka biyu na Majalisar…

Jam’iyya mai mulki ta APC da babbar jam’iyyar hamayya ta PDP sun sa kafar wando daya kan sabuwar Dokar Zabe da zauruka biyu na Majalisar Dokoki ta Kasa suka yi wa garanbawul, kuma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ki ya rattaba hannu a kai.

Wannan mataki da Shugaba Buhari ya dauka ya sa jiga-jigan jam’iyyun biyu suna zargin juna da shirin tafka magudi a zabubbuka masu zuwa.

Shugabannin Jam’iyyar APC sun zargi na Jam’iyyar PDP da hada baki da shugabannin Majalisar Dokoki ta Kasa wajen canja wasu ka’idoji da suke cikin Dokar Zabe ta shekarar 2010 (da aka gyara), domin cimma wani buri ba don karfafa tsarin dimokuradiyyar Najeriya ba.

Dokar Zaben wata doka ce  da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ne kadai ya fi ta karfi. Dokar ita ce Hukumar Zabe ta Kasa ke amfani da ita wajen gudanar da ayyukanta ba tare da samun matsaloli ba.

Wannan doka  an canja ta har sau uku, a shekarun 2004, 2006 da 2010.

Shugabannin Majalisar Dokokin Sanata Bukola Saraki na Dattawa da Yakubu Dogara na Wakilai sun fara yunkurin canja dokar da ake amfani da ita a yanzu ne tun shekarar 2016. Wannan shi ne karo na uku da Shugaba Buhari yake yin biris idan aka kai masa dokar ya sanya mata hannu; hakan ya nuna irin yadda ake zaman doya da manja a tsakanin Bangaren Zartarwa da na Majalisa.

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da na Majalisar Wakilai Yakubu Dogara, suna daga cikin wadanda aka zabe su a karkashin Jam’iyyar APC, amma suka canza sheka zuwa Jam’iyyar PDP a watannin baya.

Majiyoyi masu karfi sun shaida wa Aminiya cewa Shugaba Buhari ya ki rattaba hannunsa ne a wannan sabuwar doka ta zabe saboda shawarwari da wadansu lauyoyi da magoya bayansa da wadansu daga cikin mambobin Jam’iyyar APC a majalisun biyu da kuma shugabannin Jam’iyyar APC suka ba shi.

Duk da cewar Shugaba Buhari ya bayar da wasu dalilai, kamar cewa fara amfani da dokar a zabubbukan da za a gudanar a wata biyu masu zuwa ka iya kawo cikas da rudani. Binciken Aminiya ya gano cewa babban dalilin da ya sa Shugaban ya ki sanya hannun shi ne, an gano wani shiri da Jam’iyyar PDP da dan takararta na Shugaban Kasa, Atiku Abubakar suke yi ne domin aikata magudin zabe.

Tuni dai jam’iyyun biyu suke ta musanyar yawu da batanci ga juna kan wannan batu, inda Jam’iyyar PDP a karkashin jagorancin Yarima Uche Secondus ke zargin Shugaban Jam’iyyar APC Kwamared Adams Oshiomhole da cewa shi ne kanwa uwar-gami, domin wai yana daga cikin jiga-jigan da suka bai wa Shugaba Buhari shawarar kada ya rattaba ga sabuwar dokar zaben hannu har ta zama dokar da za a yi amfani da ita.

A ranar Juma’ar da ta gabata 3 ga Disamban bana, Shugaba Buhari ya aike da wasiku biyu ga Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki da Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara; inda ya shaida musu cewa ba zai rattaba hannu a kan kudirin ba domin yin hakan zai iya kawo cikas a shirin zabubbukan da za a gudanar a badi.

Za a gudanar da zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Dokoki ta Kasa na a ranar 16 ga Fabrairun badi; sa’annan a gudanar da zaben gwamnoni da na majalisun jihohi a ranar 2 ga watan Maris na badi.

Dalilin da rikicin ya yi kamari

A makon jiya, Atiku Abubakar, da Uche Secondus da Bukola Saraki da wadansu manyan ’ya’yan Jam’iyyar PDP da masu kokarin ganin Atiku ya kayar da Buhari a badi, sun yi wani taro a Legas da masu ruwa-da-tsaki a lamarin siyasa da fashin baki, inda suka shaida musu cewa sun gano dalilin da ya sa Shugaba Buhari ya ki ya sanya hannu a sabuwar Dokar Zaben.

Sun cewa Shugaban yana so ne magoya bayansa da kuma Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) su tafka magudi a lokacin kidaya kuri’un da za a kada a zabubbukan da za a gudanar, ta yadda Jam’iyyar APC za ta samu rinjaye.

A tsohon tsarin zabe dai, an bayar da damar amfani da takardu da fom-fom alkalami wajen tantance masu zabe a duk lokacin da na’urar zabe ta kadirida ta kasa aiki.

Sai majalisun biyu a karkashin Saraki da Dogara sun canja wannan tsari; inda suka yi sabuwar doka da ta ce duk lokacin da wannan na’ura ta kasa aiki har kimanin sa’a uku, to a soke zaben da ake shirin gudanarwa a wurin; san’annan tilas ne Hukumar Zabe ta Kasa ta sake tsara wani zabe a cikin awa 24.

A lokacin da yake tofa albarkacin bakinsa kan wannan batu, Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce hakika za su yi amfani da  na’urar tantance masu zabe a wuraren kada kuri’a sama da dubu 120 a fadin kasar nan.

Farfesa Yakubu ya ce ba za a samu matsala ba koda Shugaban Kasa bai rattaba hannu a sabuwar Dokar Zabe ba, ganin cewa za su iya amfani da tsohuwar dokar da ake da ita, wacce da ita ce aka yi amfani a zabubbukan shekarar 2015; wanda Farfesa Attahiru Jega ya gudanar kuma ake ganin shi ne zaben da ya fi kowane inganci tun dawowar mulkin dimokuradiyya a 1999.

Damuwar Jam’iyyar APC

To sai dai jam’iyya mai mulki ta APC ta ce ba wannan tsari ne abin tsoro ba; domin ta san muhimmancin na’urar tantance masu kada kuri’a; ganin cewa ita ce ta taimaka Shugaba Buhari ya kayar da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan a zaben da aka gudanar a shekarar 2015.

Wata majiya ta bayyana wa Aminiya cewar Fadar Shugaban Kasa da Jam’iyyar ACP sun bankado wata almundahana ce a sabuwar Dokar Zabem. Abin da suka bankado shi ne wani sakin layi da ya ce tilas Hukumar Zabe ta rika bayyana sakamakon zabe kai-tsaye ta yanar gizo a lokacin da ake gudanar da zabe a fadin kasar nan.

Wannan canji da ’yan majalisa suka kirkiro, shi ne babban dalilin da Shugaba Buhari ya ki ya sanya hannu a sabuwar dokar.

Wadansu na kusa da Shugaban Kasa da kuma ’yan jam’iyyar a Majalisar Dokoki ta Kasa sun ce shugabannin Jam’iyyar PDP da kuma na kusa da dan takararsu na Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, sun gayyato wasu kwararru daga kasar Isra’ila domin su shiga yanar gizon Hukumar Zabe su saci bayanai a lokacin zaben.

Majiyoyin sun kara da cewa in har aka sanya hannu a sabuwar dokar, wacce ta tanadi cewar tilas a bayyana sakamako a yanar gizo, to Turawan da aka kawo daga Isra’ila za su iya canja sakamakon zaben ta yadda Shugaba Buhari da sauran ’yan takara za su sha kasa.

Aminiya ta tuntubi Hukumar Zabe kan wannan batu, inda Kakakin Shugaban Hukumar, Mista Rotimi Oyekanmi, ya ce suna iyakacin kokarinsu ganin cewa hakan bai faru ba.

“Mu ma ba barci muke yi ba, a kullum muna canja tsarin ayyukanmu wajen amfani da na’urorin zamani. Bayan haka kuma a badi za mu yi amfani da takarda da alkalami wajen tattara sakamakon zabe, ba wai kwamfuta kadai ba.

“Don haka duk wanda yake ganin zai yi magudi to ya canja tsari domin ba zai yi nasara ba,” inji shi.

A martanin Jam’iyyar PDP kan wannan batu, Kakakinta Kola Ologbondiyan, ya bayyana wa Aminiya cewa sharri kawai ake  yi musu. “Jam’iyyar APC ta riga ta karaya, shi ya sa suke kuka tun kafin ranar da za su sha kasa; babu wani magudi da za mu yi, mun tabbata ’yan Najeriya sun gaji da APC, mu za su zaba.

“Babu wani shiri da muke yi na shiga yanar gizon INEC domin mu yi magudi,” inji shi.

Amma Kakakin APC, Malam Lanre Issa-Onilu, cewa ya yi babu abin da PDP ba za su aikata ba, domin su kwace mulki. “Muna sane da duk wani shiri da suke yi amma ba za su yi nasara ba,” inji shi.

Kan ’yan majalisa ya rarraba

Tuni dai kan ’yan Majalisar Wakilai ya rabu kan wannan batu, domin ’ya’yan Jam’iyyar APC a majalisar sun ce za su kare matsayin da Shugaba Buhari ya dauka kan sabuwar dokar. Shugaban Masu Rinjaye, Femi Gbajabiamila, a wani taro da ya gabatar a shekaranjiya Laraba, ya ce suna shirye su dakatar da duk wani yunkuri da ’yan majalisar ’yan PDP za su yi domin bijire wa matakin da Buhari ya dauka.

“Mu mun tabbata ’yan PDP ba su da yawan da za su canja matakin da Shugaba Buhari ya dauka,” inji shi.

’Yan Majalisar Wakilai dai tilas su samu goyon bayan ’yan Majalisar Dattawa kafin su canja duk wani mataki da Shugaba Buhari ya dauka, sa’annan ganin cewar shekara ta zo karshe za su tafi hutu, za su iya tilasta wa Shugaba Buhari ne kawai idan sun dauki mataki tsakanin ranar Talata mai zuwa ranar Alhamis kafin su tafi hutun Kirsimeti da sabuwar shekara.

Shi ma da yake tarfa yawun bakinsa, Farfesa Ishak Akintola, Babban Daraktan Kungiyar Kare Hakkin Musulmi (MURIC), ya ce ’yan majalisar sun saka son rai a sabuwar Dokar Zaben.  “Jam’iyyar PDP da ’yan majalisarta ba sa nufin alheri; in ba haka yaya za su canja doka a lokacin da zabe ya riga ya zo? So suke su kawo rudani domin su kwace mulki,” inji shi.