✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda bikin maulidin bana ya kayatar a Bauchi

Ranar 12 ga watan Rabi’u Auwal, dandazon miliyoyin al’ummar musulmi a fadin duniya, sukan fito domin nuna murnarsu da zagayowar ranar da aka haifi fiyayyen…

Ranar 12 ga watan Rabi’u Auwal, dandazon miliyoyin al’ummar musulmi a fadin duniya, sukan fito domin nuna murnarsu da zagayowar ranar da aka haifi fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).

Shaikh Dahiru Usman Bauchi shi ne ya jaogaranci shirya gagarumin maulidi da ya samu halartar dubban al’ummar musulmi daga ciki da wajen Najeriya inda suka taru a filin wasa na Sa Abubakar Tafawa Balewa a Jihar Bauchi.

A lokacin taron, shehin ya karanta tarihin rayuwar Manzon Allah SAW sannan ya hori al’umma da su zauna lafiya da juna, “mu ba mu da zabi, Allah shi ne Ya fimu iya zabe. Allah Ya zaba mana shugabanni na kirki Allah Ya ba mu lafiya da zama lafiya. Kullum jariri da ke bayan uwarsa yana mana wa’azi, mu lura da wa’azin, da yake mana in yana goye a bayan uwarsa in ka zo ka mika hannu za ka daukeshi, sai yaki don bai sanka ba, amma in ya ga wanda ya sani da gudu zai zo. Kaima mai yin zabe ka lura da mutumin da yake zuwa wajenka kafin zabe mai zuwa. Kowa ya yi aiki da hankalinsa mu roki Allah zabi, ka zabi wanda zai yanka maka zakaranka ko ka zabi wanda zai yanka maka wukarka. Kuri’arka wukarka, mu yi amfani da kuri’armu yadda ya dace.”

Shugaban Kungiyar Riyalul Islam da ke kula da Makarantun Islamiyya na Jihar Bauchi wadda karkashinta ake gudanar da maulidin, Alhaji Ibrahim Ahmad Baba Karami ya gode wa Allah da Ya sake nuna mana wannan rana kuma ya bayyana cewa anyi tsari mai kyau a bana domin a kara sawwaka wa jama’a saboda yadda al’umma ke karuwa kowace shekara.

Tun da karfe bakwai na safiyar ranar Talata ce dai aka fara shiga sahun muzaharar maulidin, inda daliban makaratun islamiyyoyi suka shiga gaba wajen zagayen gari da aka fara daga cikin filin kwallon Kobi. Sannan Kungiyar ’yan uwa musulmi da aka fi sani da ’yan shi’a suka mara musu ba.

Mai Martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu da Gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar sun shiga sahun ’yan kallon maulidin inda suka zauna a fadar Mai Martaba suna kallon suna kuma karbar gaisuwa  daga masu wucewa.

Gwamnan Jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar ya bayyana cewa, “ina muku godiya a bisa yadda kuke gudanar da harkokinku a jihar Bauchi ba tare da takalar wani ba, ana yin komai cikin lumana, gwamnatin jihar Bauchi tana sane da wannan shi ya sa ita ma gwamnatin take bin dukkanin hanyoyin da suka dace don ya kasance kuma ta mara muku a matsayinku na ’yan kasa na gari masu son zaman lumana,” inji shi. Sanna ya taya musulmi murnar zagowar wannan rana.

Shaikh Kabiru Al-Arabiy mai almajirai wanda yana daga cikin wadanda suka yi zagayen maulidin ya bayyana cewa maulidin Annabi aba ce mai matukar muhimmanci ga jama’an musulmi, “tarihi ne yake maimaita kansa kimanin shekara 1450 wasu sahabbai da suka fi kowa kima da daraja suka zagaye Madina a kafa suka yi zufa saboda Manzon Allah ya bar Makka ya zo garinsu, sun gane shi ne Nabiyun Rahmati, Nabiyun Barakatu, Nabiyul Khairi ne.

“Don haka wannan zagayen gari na mauludi da muke yi yau tsofansa a duniya shekara 1450 domin a ranar hijira ne suka yi masa, bayan hijira da shekara 10 Annabi ya bar duniya. Daga lokacin hijira zuwa yau shekara ne 1440 ne.

Ya kara da cewa, “Wannan muzahara ta mauludi sirrinta ita ce a fada wa duniya Annabi fa yana nan, masu ganin Annabi ya tafi iliminsu ne ya yi karanci, Annabi yana cewa babu mai tsayawa a kabarina ya yi min sallama face an fada min sunansa kuma na mayar masa sallama. Ai macacce ba ya amsa sallama, a takaice wannan muzaharar rakiya muke yi, duga-dugan sahabbai muke son mu taka.”

A nasa jawabin, Shugaban ’Yan Uwa Musulmi, almajiran Shaikh Ibrahim Zakzaky na jihar Bauchi, Malam Ahmad Yashi ya ce sun fito ne domin nuna soyyyarsu ga Annabin tsira, “abin da ya fito da mu shi ne mu tuna da ranar haihuwar Annabin Muhammad. Wannan rana ce da ya kamata kowane musulmi ya dauke ta a matsayin ranar hadin kai.”

Da yake tofa albarkacin bakinsa, shugaban kabilar IGBO mazauna Bauchi, Rabaran Dominic Nkwocha ya nuna gamsuwarsa bisa yadda musulmi ke rungumar zaman lafiya da koyi da rayuwar Annabi a jihar ta Bauchi. Ya bayyana cewar Annabi ya zo da zaman lafiya, don haka suna zaune da jama’ar musulmi a jihar lafiya.