Daily Trust Aminiya - Yadda gasar Firimiyar Najeriya ke gudana a bana
Subscribe

Yadda gasar Firimiyar Najeriya ke gudana a bana

A ranar Lahadin da ta gabata ce aka fafata wasa na 18 a gasar Firimiya ta Najeriya ta bana, duk da cewa akwai kungiyoyin da suke da kwantan wasanni da suka buga wasa 17 maimakon 18 da wadanda suka buga wasa 12 kacal.

Kungiyar Plateau United ce ke kan gaba, inda take saman teburin gasar da maki 32 a wasa 18, sai Kungiyar Lobi Stars ta Makurdi da ke biye mata da maki 31 a wasa 17,wanda idan ta buga kwantan wasanta, ta yi nasara za ta iya komawa ta daya, idan ta yi kunnen doki, ta zo daidai da Plateau United, sai dai yawan kwallaye ya bambanta su.

Bayan wasan 18, Plateau United na da bambancin kwallaye 15, Lobi Stars kuma na da 10 a wasa 17.

Kungiyar Ribers United ce ta uku da maki 29 a wasa 18.

A kasan tabur kuma, Adamawa United ce ta karshe da maki 14 bayan wasa 18, sai kungiyar Enyimba ta Abiya da ke da maki 15 a wasa 12, sai Rangers United ita ma mai maki 15 a wasa 12, sai kuma Nasarawa United mai maki 16 a wasa 17.

Kungiyoyin Enyimba na Aba da Rangers United sun buga wasa 12 ne dukkansu a cikin wasa18.

Sun samu kwantan wasanni ne kasancewar suna wakiltar Najeriya a wasannin Zakarun Afirka Afirka.

Kuma saboda suna da kwantan wasa shida-shida, ta yiwu bayan sun buga wasannin yanayin teburin yana iya canjawa.

A da can, a gasar Firimiyar ta Najeriya, abu ne mai wuya wata kungiya ta samu maki a gidan wata, ballantana a doke wata kungiya a gidanta.

Amma a kakar bana ta gasar, an samu sauye-sauye da dama, inda ake zuwa har gida a doke kungiya, ko kuma a yi kunnen doki.

Ba a kakar bana aka fara samun wannan ci gaban ba, amma al’amarin ya kara samun tagomashi sosai ne a bana.

A wasa na 18 da aka fafata, Kungiyar Dakkada FC ta yi kunnen doki a gidan Wikki Tourist na Bauchi a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa.

Haka a Jihar Anambra, Kungiyar Akwa United ta rike Kungiyar Ifeanyi Ubah a gidanta, inda aka tashi wasan babu ci. Kuma a wasa na 17, an samu kunnen doki guda uku a wasanni daban-daban.

A wasa na 16, an samu kunnen doki da dama, sannan Kngiyar Warri Wolbes ta bi Nasarawa United har gida ta doke ta da ci 2 da 1.

Haka a wasannin farko-farkon kakar ta bana, an rika samu sakamakon bazata a gasar. Kuma har yanzu zai wuya a iya cewa kungiya kaza za ta iya lashe gasar.

Yanzu kallo ya koma sama, inda Plaeau United ke ta kokarin ci gaba da kasancewa a saman teburi, domin lashe gasar, sannan Lobi Stars na ci gaba da matsa mata lamba don karbe kambin.

Sannan Enyimba da Enugu Rangers United da yanzu suke karkasin teburi, duk lokacin da hankalinsu ya dawo kan gasar, suka buga kwantan wasanninsu suna iya jirkita fasalin teburin gasar.

texem
More Stories