✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda nake kasuwancin koyar da girke-girke ta Intanet – A’isha Auyo

A’isha Musa Auyo matashiyar ’yar kasuwa ce da take koyar da girke-girke a Intanet. A hirarta da Aminiya ta fadi yadda take hada ayyukan kasuwanci…

A’isha Musa Auyo matashiyar ’yar kasuwa ce da take koyar da girke-girke a Intanet. A hirarta da Aminiya ta fadi yadda take hada ayyukan kasuwanci da karatu da fadi-tashin rayuwarta inda ta bukaci mata su kware a girki don jin dadin aurensu:

 

Mene ne takaitaccen tarihinki? 

Sunana A’isha Musa Auyo, an haife ni ranar 22 ga Fabrairu, 1999,  a Karamar Hukumar Auyo.  Na yi makarantar firamare da sakandare da kuma makarantar  Islamiyya sannan na yi karantu a Sashen Haddar Alkur’ani a Jamiar Bayero ta Kano. A lokacin mukan je makarantar boko da safe, mu je makarantar Islamiyya  da yamma a ranakun karshen mako kuma  hadda muke zuwa. Na yi digiri na farko a a Jami’ar Bayero, Kano daga shekarar 2008 zuwa 2012 inda na karanci fannin Kimiyyar Halittu masu rai da tsirai wato (Biology Education), bayan na kammala ina jirar zuwa hidimar kasa sai na shiga makarantar koyon girke-kirke  da karbar baki na yi karatun  wata shida.

Kasancewar  ni ce babba a gidanmu tun ina karama nake taya mahaifiyata girki, sannan duk sa’ar da babanmu ya kai mu wurin sayar da kayan tande-tande da makulashe a karshen mako idan muna dawowa gida sai  in gwada yin abubuwan da muka sayo da kaina. Domin ina matukar kaunar girke-girke, wannan ne  ya sa mahaifiyata ta kai ni makarantar koyon girki.

 

Yanzu kina girke-girke ke nan?

Yanzu ina kasuwancin girke-girke ne da ake kira ‘catering’ wato ina koyar da girke-girke ta kafar Intanet wato  online. Sannan ina koyarwa a ajujuwa a zahiri. Nakan shigo da kaya daga kasar China amma yanzu saboda karatuna girke-girken kawai nake samun damar yi. Abu ne mai kyau mata su nemi na kansu, aikin zuwa ofis ko yin kasuwanci, amma kada neman kudi ya sa a shiga hakkin kula da miji ko yara, domin wannan shi ne abu na farko mafi a’ala. Sannan  kada mu manta da kula da lafiyarmu da  farin cikinmu  da ci gabanmu.

Na san fada ya fi cikawa sauki, wannan ne dalilin da ya sa na yi rubutun digirina na biyu  kan yadda mace za ta hada hidimar gida da ta aiki da kula da kanta, ba tare da ta shiga hakkin kowanne ba. Kuma ina rokon maza da ’yan uwa da iyaye su yi hakuri su taimaka wa mata masu zuwa makaranta  ko aiki saboda suna matukar bukatar haka.

 

Yaya kike kula da aure da ci gaba da karatu?

An yi mini aure a shekarar da na kammala digirin farko wato 2012,  bayan na kammala karatun Koyon Girke-Girke da Karbar Baki.  Bayan na yi aure da wata biyu,aka kira ni zuwa hidimar kasa (NYSC), inda na yi aikin a Jami’ar Bayero. Bayan nan a shekarar 2014  na fara karatun digiri na biyu a bangaren Halayyar dan Adam (Psychology of Education) a Jami’ar Bayero. Da na hada karatun a shekarar 2018 sai na ci gaba inda  yanzu nake yin karatun digiri na uku wato digirin digirgir a bangaren Sanin Halayyar dan Adam (Psychology of Education).

Zan iya cewa duk rayuwata tun daga haihuwa da karatuna a sashen gidajen ma’aikata na Sabuwar Jami’ar Bayero na yi ta har da  mijin da na aura shi ma a rukunin gidajen ma’aikatan jami’ar yake, kasancewar iyayenmu ma’aikatan jami’ar ce.

 

Ta yaya kika hadu da mijinki?

Na hadu da mijina a nan sabuwar Jami’ar Bayero tun ina karama, domin makwabtanmu ne, amma ba mu fara soyayya  ba sai sada na cika shekara 18, ina aji na 2 a jami’a, mun samu fahimtar juna ne lokacin da muka yi aikin koyar da hadda a Makarantar Haddar Alkur’ani  wato Mukurra’ul Mustakbal da ke Jami’ar Bayero. Aure ya ba ni damar fita daga rukunin gidajen Jami’ar Bayero zuwa wasu jihohin kasar nan, domin na zauna a Kaduna daga shekarar 2013 zuwa 2017 daga nan muka koma Abeokuta a Jihar  Ogun inda na zauna daga shekarar 2017 zuwa 2019, yanzu haka muna zaune a garin  Idiroko da ke iyakar Najeriya da kasar Benin a Jihar Ogun.

Wannan yawon daga wani sashe na kasar nan zuwa wani ya ba ni damar kara ilimin gogayya a rayuwa inda na hadu da jama’a da dama masu bambanci al’adu maimakon a baya da rayuwar da na sani ba ta wuce ta harabar Jami’ar Bayero, Kano ba,

Sannan hakan ya ba ni damar fadada kasuwanci inda nakan yi odar kayayyaki daga kasashen ketare. Sannan na kara samun gogewa a sana’ata ta girke-girke kasancewar ana yin bukukuwa a Kudancin kasar nan fiye da Arewa.

 

Mene ne kika fi so game da mijinki?

Gaskiya abin da ya ja hankalina game da shi, shi ne; shi mutum ne mai addini da tarbiyya, sannan zuciyata ta fi kwanciya da aurar wanda muka tashi tare ta yadda ba za mu samu matsalar zamantakewa ba. Mutum ne  jajirtacce mai yawan kwazo da ba ya gazawa a ayyukan da ya sa gaba ko aka sa shi.

Yana son karatu, don haka ra’ayinmu  ya zo daya. Ga shi  kuma yana son yawon bude-ido da karo ilimi, don haka mukan yi tafiye-tafiye tare, duk da yana son aikinsa amma yana bai wa rayuwar iyalansa fiffiko da matukar muhimmanci.

Yana matukar taka rawa ga samun nasarorina, shi yake ba ni kwarin gwiwar yin karatu da kasuwancina na girke-girke. Yana  fifita nasarata da ci gabana a kan jin dadinsa, domin duk abin da ya shafi karatuna sai  inda karfinsa ya kare.

 

’Ya’yanku nawa a yanzu?

Allah Ya albarkace mu da ’ya’ya biyu maza.

 

Ya kike ji a matsayinki ta mahaifiya? 

Kasancewata mahaifiya babban mataki ne da na taka a rayuwa wanda hakan ya sa na zamo mai juriya da jajircewa da karin hakuri da kuma girmama iyayena da duk na gaba da ni. Kullum ina gode wa Allah da Ya ba mu ’ya’ya masu lafiya da kokari, babban burina shi ne su kasance yara nagari, masu yawan ilimi da sa’a, sannan su kasance abin alfaharin Manzonmu Annabi Muhammad (SAW).

Alhamdulillahi iyayena sun yi mini matukar kokari wajen kulawa da, tarbiyyata tare da ba ni ilimin boko da addini. Sun kuma  haifo min kanne da muka  taso cikin so da kaunar juna. Kuma na ji dadin yadda suka  bar ni na auri wanda zuciyata ke so da kauna  duk da ina da manema cikin ’yan uwansu amma suka kyale ni na auri wanda nake so.

Kin yi maganar tura ki makarantar koyon girke-girke da mahaifiyarki ta yi bayan ta lura kina da sha’awa ko akwai wani muhimmanci da girki ke da shi ga mata?

Eh, girki na da matukar tasiri da taka rawa a rayuwar aure, wannan ne ya sa ake karin magana cewa hanyar rayuwar mutum shi ne cikinsa. Idan mace ta iya girki ta samu wurin zama a zuciyar mijinta, ba ta da damuwar miji ya je wani wuri ya ci abinci.

Ta san ba zai samu kamar nata ba, sannan kwarewa a girki na ba miji kwarin gwiwar kawo baki da ’yan uwa zuwa  gidansa. Ba ma miji kawai ba, kwarewa a sarrafa abinci yana taimaka wa iyalai wurin samun lafiya, don haka wajibi ne mace ta maida hankali wajen koyon girki domin kyautata zamantakewar aurenta.

 

Mece ce nasaraki a rayuwa?

Babbar nasarata a rayuwa ita ce samun ilimin addini da na boko a shekaru kalilan. Tun daga Islamiyya da karatun boko daga firamare har zuwa digirin digirgir, nakan samu kaina a mafi kankantatar shekaru a ajujuwan da na yi karatu. Yanzu haka duk wanda ya gan ni sai ya yi mamakin cewa ina karatun digirin digirgir ne a shekaru kasa da talatin. AlhamdulilLahi, Ubangiji Shi ne abin godiya, sannan iyayena da kuma mijina wadanda burinsu shi ne ci gaban rayuwata.

 

Ko akwai wata shawara da za ki ba mata ’yan uwanki? 

Shawarata ga mata abin da ya fi komai muhimmanci a rayuwa shi ne iyali. Duk matsayin da mace ta tsinci kanta, ta sani cewa iyalinta su ne mafiya muhimmanci. Yi wa  miji biyayya da kyautatawa ba kauyanci ba ne, komai iliminki da dukiyarki Aljannarki na karkashinsa. Sannan ko a zaman duniya ma za ki samu riba.

Abu na biyu shi ne karatu bayan aure duk da a hakikanin gaskiya karatu da aure yana  da wahala, ba kamar lokacin da mutum ba ya da aure ba. Amma in an yi dace da miji mai fahimta  komai yakan zo da sauki. Haka zalika ’yan uwa ma suna taka rawar gani sosai. A nawa bangaren na samu fahimta  sosai da maigidana saboda lokacin da na yi karatun digiri na biyu muna Kaduna da zama, haka ya hakura na taho Kano na koma gidanmu inda aka bai wa yaron da na haifa na farko kulawa sosai. Wannan ya sa na samu damar maida hankali a karatuna, har na samu yawan makin da a baya  lokacin da ban da aure ban samu ba.

Haka yanzu da nake karatun digirin digirgir dana na biyu kannena ke kula da shi har ya shiga makaranta, sannan mijina ya yi hakurin mu taho Kano in yi karatun duk da muna Jihar Ogun da zama.

Iyayen mijina su ma suna yi min kokari wajen taya ni hidimar yara da abincin da za mu ci, idan muka dawo daga makaranta a gajiye. Da irin wannan kulawa da taimako matar aure za ta yi karatu cikin natsuwa fiye da wadda ba ta da aure don haka mata kada mu yarda a bar mu a baya.

 

Yaya kike yin hutu?

Yadda nake hutuwa shi ne in samu wuri mai tsabta, cike da kanshin turaren wuta in zauna, in sha shayi, sannan in yi karatu ko na Kur’ani ko karatun litattafan zube ko na bincike. Abin da na fi so shi ne ina karatu ina shan shayi.

 

Mene ne burinki a rayuwa?

Burina a rayuwa shi ne, in zama sananniyar malama, masaniya, ina matukar son aikin koyarwa da nazari tare da gudanar da bincike.  Idan Allah Ya ba ni dama ina son tallafa wa nakasassu da masu tabin hankali domin iyaye masu irin wannan yaran suna matukar ba ni tausayi ganin yadda suke jajircewa da yin ayyuka tukuru a kansu. Domin ’ya’ya masu nakasa na bukatar kulawa ta musamman fiye da takwarorinsu masu lafiya. Sannan ina so in iya Larabci sosai.

Ko kin shiga a dama da ke a kungiyoyi?

Kwarai kuwa domin ina cikin wasu kungiyoyin ci gaban al’umma da suka hada da Kungiyar FAYOHI wacce take bincike a kan lafiyar iyali da matasa sai kuma Kungiyar SCE a Jami’ar Bayero  wacce  kungiya ce da take Afirka bisa taimaka wa matasa masu bincike da rubutu.