✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda wasan kokawa ya gudana a Bikin Al’adun Hausa a Burkina Faso

Kokawar gargajiya tana daya daga cikin wasannin al’adun Hausawa na Duniya karo na biyu da aka gudanar a makon djiya a Wagadugu babban birnin kasar…

Kokawar gargajiya tana daya daga cikin wasannin al’adun Hausawa na Duniya karo na biyu da aka gudanar a makon djiya a Wagadugu babban birnin kasar Burkina Faso.

’Yan kokawa daga kasashen Nijar da Togo da sauransu ne suka shiga cikin wasannin.

Wadannan wasanni an yi su ne a wani bangare na gudanar da bikin al’adun Hausa na kasa da kasa wanda gamayyar kungiyoyin da suka fito daga kasashen Afirka 18 suka hadu a karkashin kungiyar Makaranta da ke Burkina Faso bisa jagorancin Na-Garba Abdurrahman.

An gudanar da wasannin gargajiya da suka hada da wasan wuta na makera da wasan wanzanci da raye-raye da wake-wake.

Cikin wadanda suka cashe a wajen bikin har da mawakiyar Hausa ta zamani Fati Nijar, inda ta wake harshen Hausa da kuma ita kanta kasar ta Burkina Faso.

Ta fuskar wasan kokuwa kuwa wanda ya zama wasa na karshe a wajen gudunar da wannan biki na al’adun Hausa na kasa da kasa, ’yan Tawirgen sun fafata a tsakaninsu. Wasa biyu ne wanda ya fi burge jama’a a tsakanin Damisa da abokin karawarsa Muhammadu wadanda kuma ’yan-uwan juna ne.

Wasan da bai yi kaye ba sai da aka yi Sallar Magariba aka dawo sannan aka ci gaba.  A karshe sai sulhu aka yi, Muhammadu ya bai wa Damisa nasara kasancewarsa shi ne karami.

Sai wasa a tsakanin Habibu Idris da Umaru Musa. Abin da ya fi burge ’yan kallo a wannan kokawa shi ne yadda kowane ya fito kamar zai cinye abokin karawarsa, ba kamar Umaru wanda ya yi tsaye yana ta kirari amma ana raba rana,sai ga kafafuwan Umaru a sama, Habibu ya raba shi da kasa kafin ya kayar da shi. Wannan kokuwa ta burge ’yan kallo musamman yadda Umaru ya mike a makake yana son su koma turmi na biyu.