Search
Subscribe
Yadda ’yan mata 9 suka rasu a hadarin kwale – Kwale

Yadda ’yan mata 9 suka rasu a hadarin kwale – Kwale

Wadansu ’yan mata 9 sun rasu a wani hadarin kwale-kwale da ya rutsa da su a Kogin Tudun Iya da ke Gundumar Wuciciri a Karamar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna.

Hadarin ya faru ne a ranar Juma’a mako biyu da suka gabata da misalin karfe12 na rana, a  hanyarsu ta komowa gida daga Hayin Sarkin Fito. Aminiya ta gano cewa, ’ya matan sun kai gabar da za su tsaya sai kwale-kwalen ya kife da su, yayin da sauran abokan tafiyarsu bakwai suka tsira da rayukansu.

Wadansu daga cikin ’yan matan da hadarin ya rutsa da su kuma suka tsira, Fatima Idris da Fai’za Abdullahi, wadanda daliban makarantar Islamiyya ne a garin Maganda kuma kawayen juna ne da wadanda suka rasun sun yi wa Aminiya bayani yadda lamarin ya faru.

“Mun je Hayin Sarkin Fito ne yadda muka saba domin kalar dankali, to sai hadari ya hadu, ruwa ya zo gadan-gadan don haka sai muka kamo hanyar dawowa gida. Muna zuwa bakin kogi sai muka tarar da yaron mai kwale-kwale ne a bakin kogin. Sai ya ce mu raba kanmu biyu saboda iska ta fara kadawa kuma an fara ruwa. Sai kowa ya ki yarda a bar shi a baya, don haka muka shiga cikin kwale-kwale  dukkanmu tare da kayanmu.

Har mun kusa kai wa gaba sai iska ta fara juya mu, kwale-kwale ya fara kamfatar ruwa yana tagal-tangal. Sai muka fara kiran dan uwan mai kwale-kwalen, cewa ya zo ya taimaka mana. Sai ya ce ai ba abin da zai iya yi. Kafin kwabo jirgin ya fara cika da ruwa, ganin haka sai daya daga cikinmu ta yi tsalle ta fada ruwan. To daga nan sai kwale-kwale ya nutse da mu, kowa sai ta kai-ta kai ke yi,” inji ta

Ta ce, “Daga nan Allah Ya kubutar da mu, domin cikin mu 16  da muke cikin kwale-kwalen, mu bakwai ne kawai muka tsira, duk sauran su rasu.”

Daya daga cikin iyayen yaran da ya rasa ’ya’ya biyu a hadarin, Malam Adamu Yahaya Maganda ya ce: “Na rasa ’ya’ya biyu, Khadijatu mai shekara 13 da kanwarta Zainabu, wadda aka fi sani da Ummi, mai shekara 11. Kamar yadda ka sani ne, a wannan karkarar yaranmu sukan yi zuga domin zuwa neman abin masarufi, yin itace ko aikin shuka ko sa taki a gonaki, ana ba su dan abin hasafi. To na dawo gida ganin cewa hadari ya taso, sai na tambaya ina suke sai aka ce suna Hayin Kogi ba su dawo ba. Duk da cewa babu wani abu da ya taba faruwa a kauyenmu mai kama da haka amma na kasa samun natsuwa saboda ruwan da ake tafkawa, ana cikin haka sai muka fara jin kururuwa cewa a kawo dauki, yara sun nutse a ruwa, gari ya rude. Aka bazama nema, cikin wadanda ba a gansu ba har da ’ya’yana biyu. To, nan take na yanke jiki na fadi saboda damuwa, ganin cewa ita dayar har an samar mata Makarantar Jama’atu kuma an kammala komai; sai dai kawai ta fara zuwa, wannan abu ya faru.”

Daya daga cikin matuka kwale-kwalen ya ce duk da ba ya nan abin ya faru, ya san cewa nauyi ne ya yi wa jirgin yawa, domin tsawon shekarun da suka yi suna fito daga bakin Kogin Gangaren Gora zuwa sauran kauyakun ba su taba samun hadari ba sai wannan da Allah Ya kawo. “Don ba mu daukar mata fiye da goma a jirgin da ya nutse, saboda mata suna da nauyi ba kamar maza ba, amma idan maza ne har ma sama da haka ana dauka,” inji shi.

Ya  ce “A kullum muna fiton mutum 50 ko 70, wata rana har 100, musamman idan ana sha’ani, domin  kogin yana tsakanin garuruwa ne kamar su Wuciciri da Sabbi da Gamji zuwa Iya da Maganda da kauyen Aba da Kalandi da Kaku da Kwarin Zakara; garuruwa sun kai kusan 20 da muke hada zumuncinsu da ’yan uwa kuma kudin da muke karba ba ya wuce Naira 30 zuwa 50, kuma a zuwa da dawowa ne domin wannan ita ce hanyar da tafi sauki ga al’ummar yankin.”

Dagacin Tudun Iya, Alhaji Muhammad Musa ya ce, “A ranar da lamarin ya faru mun samu gawar yara biyar ne daga cikin tara da suka rasu, sai washegari aka sake samun gawar yara uku a wani kauye kusa da mu. To amma gawar yarinya daya, sai bayan kwana uku aka samu gawarta, a nisan kilomita 10 daga inda hadarin ya faru, har ta fara canza kama, don haka a can inda aka gan ta aka yi mata sutura.”

Ya ce yaran da suka rasu su ne Talatu Musa da Salamatu Umaru da Nasiba Sule da Naja’atu Umaru da Ruma Aliyu da Ummi Adamu da Khadijatu Adamu da Fatima Aminu, sai Hajaratu Adamu.

Dagacin ya bayyana korafinsa kan yankewar gada a yankinsa. “Gadar hanyarmu, ruwan da aka kwana yi ya yanke ta, don haka a yanzu muna kulle ne, ba mu da wata hanya da za mu shigo gari, idan da motoci ne dole mu a je mota mu koma wa babura, koda kuwa za mu kai amfanin gona ne,” inji shi.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin