Daily Trust Aminiya - Yadda ’yar Kim Kardashian ta samu kyakkyawar tarba
Subscribe

Yadda ’yar Kim Kardashian ta samu kyakkyawar tarba

A ranar Asabar da ta gabata ce kwararriyar mai gabatar da shirin talabijin, Kim Kardashian ta haifi santaleliyar yarinya a birnin Los Angeles na Amurka.
Wani abin al’ajabi da ya ba iyalinta mamaki, shi ne yadda Kim ta haifi yarinyar wata daya kafin ranar da likita ya ce mata za ta haihu. Duk da haka dai, kasancewar uwa da ‘ya suna cikin koshin lafiya, mahaifin yarinyar, Kanye West da sauran ’yan uwa da abokan arziki sun nuna matukar murna da haihuwar.
Jaririyar, wacce aka bayyana cewa tana da bakar suma wulik, ta yi kama mai tsanani da mahaifiyarta, Kim Kardashian, kamar yadda kafar watsa labarai, E- News ta ruwaito.
Tun bayan haihuwar tata a makon jiya, Kim ba ta gudanar da wasu harkoki a bainar jama’a ba, in baya ga sakonnin da ta rika rubutawa a turakunta na yanar gizo a ranar Lahadin makon. Ta saka hotonta lokacin da take makaranta sannan kuma ta taya mahaifinta, Robert Kardashian murnar ‘Ranar Uba.
Da take nuna murna da zuwan jaririya, kanwar Kim, Khloe Kardashian, ta bayyana a turakarta ta Twitter tana cewa: “Ba ba zan ma iya bayyana irin albarkar da ta shigo cikin iyalinmu ba, musamman ganin yadda uwa da jaririyar suna cikin koshin lafiya, suna hutawarsu. Muna godiya da nuna farin ciki ga dukkan wadanda suka nuna mana kauna.”
Ita kuwa mawakiya Beyonce, sakon taya murna ta aika wa Kim da mijinta Kanye West. Kamar yadda ta bayyana farin cikinta ta sakon intanet, cewa ta yi: “Ina taya ku murna, Kim da Kanye, da fatan za ku kasance cikin murna da farin cikin duk tsawon rayuwarku.”

texem
More Stories