Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

‘Yan bindiga sun kashe dan jigon PDP a Benuwe

Wasu ‘yan bindiga sun kashe dan jigon jam’iyyar PDP Yandev Amaabai, daya daga cikin tsohon shugabannin  jam’iyyar a karamar hukumar Gboko a jihar Benuwe.

‘Yan bindigar sun kashe yaron mai suna Orkuma Yandev Amaabai, ne a lokacin da yake hanyarsa ta komawa gida ranar Asabar da daddare inda `yan bindigan suka harbe shi.

ADVERTISEMENT

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Catherine Anene ya tabattar da aukuwar lamari. A yanzu haka hukumar ‘yan sandan na ci gaba da binciken kisan.

ADVERTISEMENT