✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 10 a Biniwai

Rahotanni sun ce wadansu ’yan bindiga sun kashe mutum 10 a wani sabon hari da suka kai a Unguwar Tser Uoreleegeb a yankin Ubabai da…

Rahotanni sun ce wadansu ’yan bindiga sun kashe mutum 10 a wani sabon hari da suka kai a Unguwar Tser Uoreleegeb a yankin Ubabai da ke Karamar Hukumar Guma a Jihar Biniwai.

Majiyarmu ta gano cewa lamarin ya faru ne cikin daren ranar Talatar da ta gabata, lokacin da wadanda aka kashe ke barci a kofar gidansu saboda zafi, inda ’yan bindigar na zuwa suka fara harbinsu, bayan sun kashe mutanen nan take suka tsere daga unguwar.

Shugaban Karamar Hukumar Guma, Richard Shior ya tabbatar wa manema labarai cewa, ’yan bindigar sun kai hari unguwar kuma ya tabbatar da kisan mutum 10 da suka yi.

Richard ya ce wadanda ake zargi da kashe mutanen 10, ana kyautata zaton su ne suka kashe wani mutum a ranar, kafin suka kai harin kauyen Tser Uoreleegeb.

A lokacin da shugaban karamar hukumar yake ganawa da manema labarai a Makurdi babban birnin jihar a shekaranjiya Laraba, ya ce an binne wadanda ’yan bindigar suka kashe.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Benuwai, DSP Catherine Anene, ta tabbatar wa wakilinmu ta wayar tarho cewa sun samu rahoton sabon harin da aka kai a unguwar, da take Karamar Hukumar Guma.

Ta ce zuwa yanzu da ake hada rahoton ba su tabbatar da adadin wadanda aka raunata lokacin harin ba.

Kwamandan soja da ke aikin tabbatar da tsaro a jihar, Manjo-Janar Adeyemi Yekini ya ce, jami`an tsaron na ci gaba da binciken harin da aka kai Unguwar Tser Uoreleegeb a Karamar Hukumar Guma.