✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindigar Katsina da Zamfara sun koma jihar Neja – Sanatoci

Sanatocin jihar Neja sun bayyana cewa ‘yan bindigar jihohin Katsina da Zamfara sun tare a wasu garuruwan jihar Neja, sun kuma addabi al’ummar jihar. Sanata…

Sanatocin jihar Neja sun bayyana cewa ‘yan bindigar jihohin Katsina da Zamfara sun tare a wasu garuruwan jihar Neja, sun kuma addabi al’ummar jihar.

Sanata Sani Musa mai wakiltan Neja ta Gabas, ne ya sanar da hakan inda ya ce ‘yan bindigan suna cin karansu ba babbaka a wasu yankunan jihar.

Sanata Sani, ya ce kwanan ne ‘yan bindigar suka yi garkuwa da Hakimai biyu bayan sun bankawa garin wuta, sannan sukan jikkata wasu da dama.