✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan Boko Haram sun kashe mutum 15 a Borno

Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kashe mutum 15 da wasu jami’an tsaro uku a wani sabon hari da suka kai a…

Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kashe mutum 15 da wasu jami’an tsaro uku a wani sabon hari da suka kai a karamar hukumar Kala-Balge a jihar Borno a daren ranar Litinin.

Mazauna garin da masu bada agaji sun shaidawa manema labarai cewa, jama’a da dama ne suka fice daga garin bayan da maharan suka kona gidajen jama’a da wani sassanin sojoji da ke garin Rann.