✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan gudun hijira dubu 15 daga Sakkwato, Zamfara sun koma Nijar

Hukumar bada agajin gaggawa NEMA ta ce, ‘yan gudun hijira dubu 15 daga jihohin Sakkwato da Zamfara sun tsallaka zuwa jamhoriyar Nijar, kamar yadda shugaban…

Hukumar bada agajin gaggawa NEMA ta ce, ‘yan gudun hijira dubu 15 daga jihohin Sakkwato da Zamfara sun tsallaka zuwa jamhoriyar Nijar, kamar yadda shugaban NEMA na shiyyar Sakkwato Dakta Kofoworola Soleye, ya sanar.

Dakta Kofoworola, ya bayyana hakan ne yau a Gusau babban birnin jihar Zamfara, ya ce mafi yawan `yan gudun hijirar sun fito ne daga unguwanni 27 na karamar hukumar Isa a jihar Sakkwato.

‘Yan gudun hijirar sun shiga Nijar ne ta garin Guidan Roumdji a yankin Maradi da ke makwabtaka da jihohin.