✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Kasuwar Kifi a Kano sun yi asarar mai yawa a gobara

A karshen makon da ya gabata ne gobara ta tashi a Kasuwar ’Yan Kifi da ke Jihar Kano, inda ta lakume kifi da sauran kayayyaki…


A karshen makon da ya gabata ne gobara ta tashi a Kasuwar ’Yan Kifi da ke Jihar Kano, inda ta lakume kifi da sauran kayayyaki na kimanin Naira miliyan 350, baya ga kayayyaki da wutar ta lashe, ta kuma kone tsabar kudi wanda ba a san iyakarsu ba.

Aminiya ta kalato cewa wutar ta tashi ne da misalin karfe bakwai na dare, bayan ’yan kasuwa sun tafi gidajensu, inda kuma ta dauki awoyi tana ci kafin daga bisani jami’an Hukumar Kashe gobara su yi nasarar kashe ta.

Haka kuma an bayyana cewa wutar ta tashi ne sakamakon dawo da wutar lantarki da aka yi, inda kuma wutar ta kara munana sakamakon fashewar tukunyar gas da ke jikin na’urorin firji da ake adana kifi a kasuwar.

Shugaban kungiyar ’yan kasuwar Mista Shola Majek ya kimanta halin da ’yan kasuwar suke ciki, inda ya ce kimanin mutane dubu biyu da ke yin kasuwanci a wannan kasuwa, sun rasa hanyar cin abincinsu.

Majek, wanda ya ce ya rasa kaya na kimanin Naira miliyan 25, ya roki gwamnati da ta kawo masu dauki don sake kafa kasuwancinsu.

Wani dan kasuwa, Alhaji Jibril Maikifi ya bayyana cewa tsawon shekara 18 ya dauka yana gudanar da kasuwanci a wanann kasuwa amma bai taba ganin wani abu makamancin haka ba. Ya ce ya rasa kaya na miliyoyin Naira domin a ranar da wutar ta tashi suka sauke kayan kifi tirela daya da rabi, wadanda suke cikin kwantenoni guda biyu.

’Yan kasuwar sun dora alhakin munin gobarar a kan jami’an hukumar kashe gobara ta Jihar Kano saboda rashin halartar kasuwar a kan lokaci, inda suka dauki tsawon mintuna 45 ba tare da sun zo ba. Duk kokarin Aminiya don jin ta bakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ya ci tura, sai dai wani jami’i da ya nemi a boye sunansa ya bayyana cewa a lokacin da wutar ta tashi ba su da isasshen ruwa a motocinsu, hakan ya jawo aka sami tsaiko.