✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama matsafin da ake zargi da kashe matar aure

Yan sanda a Jihar Oyo sun kama wani da ake zargin matsafi ne mai suna Dotun Ogunlade, mai lakabin ‘Aroye Jesu’ da ake zargi da…

Yan sanda a Jihar Oyo sun kama wani da ake zargin matsafi ne mai suna Dotun Ogunlade, mai lakabin ‘Aroye Jesu’ da ake zargi da kashe wata matar aure mai suna Bose Oguntunde inda ya babbaka kokon kanta da wasu sassan jikinta ya yi tsafin samun kudi ga abokin huldarsa mai suna Mutiu Ayorinde. A ranar Alhamis din makon jiya ne Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Oyo, Shina Olukolu ya jagoranci wadansu manyan jami’ansa da  manema labarai zuwa wani gidan bauta mallakar Dotun Ogunlade da ke garin Igboora inda aka yi wa matar kisan gilla.

Da yake yi wa manema labaran bayani Kwamishinan ’Yan sandan cewa, ya yi wannan mutum Dotun Ogunlade, ya yaudari matar ce ya gayyace ta daga Ilorin a Jihar Kwara zuwa Igboora domin cimma burinsa. A lokacin da matar ta iso Igboora sai mutumin ya dauke ta zuwa wannan gida ya ba ta wasu magunguna da allurar barci. A daidai lokacin da barci ya kwashe ta ne sai Dotun Ogunlade ya makure ta, sai da ya tabbatar da mutuwarta sannan ya yanke hannayenta da kokon kanta ya ajiye tare da haka rami ya binne sauran sassan jikinta.

Dotun Ogunlade bai musanta zargin aikata danyen aikin ba. “Mun jima muna tuntubar juna da wannan mata ta shafin sada zumunta na Facebook inda ta shaida min irin matsalolin da suke damunta wadanda take so in yi mata magani.

Na yi mata alkawarin shawo kan matsalarta idan ta zo wurina a garin Igboora, inda ta amince da hakan ta zo. Kafin ta zo wurina sai da wannan abokin huldata Mutiu Ayorinde, ya kawo kukansa cewa yana so a yi masa maganin samun kudi, inda ya kawo Naira dubu 30 a matsayin ladan aiki da wasu kaya da za a sayo domin biyan bukatarsa. Na kashe wannan mata,  na yi amfani da wasu sassan jikinta domin yin maganin samun kudi cikin dare daya ga mutumin ne,” inji shi.

Ya ce: “A baya na sha yi masa makamancin wannan aiki amma ya ce bai isa ba, yana bukatar fiye da wannan.”

Shi kuwa Mutiu Ayorinde, cewa ya yi, “Gaskiya ce na nemi a yi min tsafin kudancewa cikin dare daya, amma ni ban bukaci a yi amfani da sassan jikin dan Adam domin shirya maganin ba.”

Kwamishinan ’Yan sanda Shina Olukolu, ya nuna wa ’yan jarida wasu kaya da suka hada da wukake da aka yi amfani da su wajen yanke sassan jikin matar da fararen kyalle da bakin sabulu da giyar gwaggwaro da aka yi amfani da su wajen markada wannan magani.

Nan take Kwamishinan ya umarci mutanen, Dotun Ogunlade da Mutiu Ayorinde da su hake ramin da suka binne sassan jikin wadda suka kashe, inda daga nan aka kai rubabbiyar gawar wajen ajiye gawarwaki na asibitin gwamnati har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

Kwamishinan ya nuna farin cikinsa ga mutanen da suka bayar da rahoton sirri da ya kai ga bankado wannan al’amari.