✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yar shekara 13 ta haifi cikin da makwabcinsu ya yi mata ta hanyar  fyade

An yi nasarar yin tiyata wa wata yarinya mai shekara 13 (an sakaya sunanta) da ke garin Isa a Karamar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato…

An yi nasarar yin tiyata wa wata yarinya mai shekara 13 (an sakaya sunanta) da ke garin Isa a Karamar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato inda aka cire mata  dan da makwabcinsu ya yi mata hanyar fayde.                                                               \

An yi wa yarinyar aiki ne kasancewar  ba za ta iya haihuwarsa da kanta ba a asibitin Maryam Abacha da ke Sakkwato saboda karancin shekarunta.

Aminiya ta je asibitin domin jin ta bakin yarinyar kan yadda lamarin ya faru ita ganin tana tare da iyayenta, inda ta ce a wani lokaci ne kimanin wata tara, Sama’ila Mu’azu makwabcinsu da gida daya ke tsakaninsu ya nuna yana sonta, amma ba zai zo gidansu ba, “Wani lokaci na biyo zan shiga gidansu ya tura ni cikin dakinsa da ke farkon shiga ganin ya yi min abin da duk yake so, sannan ya ce in na fada sai ya kashe ni, daga nan na yi shiru ban fadawa kowa ba, ashe ciki ya shiga ban sani ba har sai da gidanmu da mutanen unguwa suka gane ina dauke da ciki,” inji ta.

Ta ce “Bayan haka ne wani dan unguwar ya tafi ya fada wa ’yan sanda na yi ciki aka bi mahaifina  gona aka kama shi aka hada da ni  aka kulle mu a ofishin ’yan sanda na Isa, daga baya aka yi belinmu kan Naira dubu 10, sai suka tura maganar kotu domin iyayena sun ce suna son a kwato min hakkina.”

Ta ci gaba da cewa a gaban alkalin kotun Isa Sama’ila ya amince ya ci amanarta kuma in ta haihu zai yi wa yaro suna ya  aure ta, har bayanin amincewa ya rubuta a matsayin shaidar zai aikata abin da ya fadi.

Kanen mahaifinsa Bello Tudu ya ce ba za a yi haka ba domin yana takama da kudi, haka ya lalata maganar a kotu, har alkali ya yanke mata hukuncin zama gidan yarin Sakkwato na wata shidda  ko biyan tarar Naira dubu shida, sai suka biya tara.

Yarinyar ta ce, “Ganin yadda lamarin ya faru a kotu mahaifiyata da kakata suka lashi takobin kwato min hakkina a Sakkwato ta hannun masu kare ’yancin dan Adam, sai aka sake rashin sa’a suka fada hannun wani matashi a garinmu Uma Mai Hoto ya ce shi ma yana aiki da kungiyoyin kare hakkin dan Adam, shi ne ya zo yana ta karbar kudinmu a matsayin kudin shari’a, kudin da nake tunawa an ba shi shi ne Naira dubu 50 a matsayin kudin daukaka kara, ya amshi Naira dubu 70 kuma, ya sake amsar Naira dubu 40 da dubu 15 sau biyu. Ya zo da ni Sakkwato wurin wasu lauyoyi 9. Ba mu gane karya yake yi ba sai da Allah Ya hada mu da wata lauya mace da ta taimaka mana, ita ce sanadiyyar zuwanmu Sakkwato har aka yi min aiki, ita ce ta dauki dawainiyarmu har zuwa yanzu da na samu sauki,” inji  ta..

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato ASP Muhammad A. Sadik ya ce sun samu labarin lamarin, kuma sun kamo yaron yana hannunusu suna ci gaba da bincike kan yadda lamarin yake, kuma bayan an kammala za su kai maganar kotu.