Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Yarinya ‘yar shekara 10 ta haihu a Benuwai

A jiya Litinin 5 ga watan Agusta 2019, wata yarinya ‘yar shekara goma da haihuwa, mai suna Masenengen Targbo ta haifi jaririya a wani asibiti da ke garin Makurdi na Jihar Benuwai.

Yarimyar, wacce aka tabbatar da cewa wani ne ya yi mata fyad’e kuma ta samu ciki duk da k’arancin shekarunta, an yi mata aikin fid’a ne aka ciro jaririyar da misalin k’arfe 1:00 na dare, a wani asibiti mai zaman kansa mai suna Foundation Hospital da ke garin na Makurdi. Jaririyar mai nauyin kilogiram 2:5 tana cikin k’oshin lafiya.

ADVERTISEMENT

Har zuwa hada wannan rahoton ba a gano wanda ya yi wa Masenengen fyaden ba.

ADVERTISEMENT