✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau kotun koli za ta yanke hukunci kan zaben Kano, Sakkwato da Imo

A yau Litinin ne kotun kolin za ta yanke hukunci bayan daukaka kararrakin zabukan Gwamnonin da suka hada da:  Gwamnan jihar Kano Umar Ganduje, Gwamnan…

A yau Litinin ne kotun kolin za ta yanke hukunci bayan daukaka kararrakin zabukan Gwamnonin da suka hada da:  Gwamnan jihar Kano Umar Ganduje, Gwamnan jihar Sakkwato Waziri Tambuwal da kuma Gwamnan Imo Emeka Ihedioha.

Majiyarmu ta samu rahoton cewa, idan akwai yiwuwar daukaka karar za a yi hakan ne bayan saurarar kararrakin zabukan Gwamnonin.

A wani bangaren kuma akwai kararrakin da aka daukaka karar su, na Gwamnoni bakwai da suka hada da:  Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Fintiri;  Gwamnan Bauchi Bala Mohammed;  Gwamnan Benuwe Samuel Ortom; da Gwamnan jihar Filato Simon Lalong.