✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Murja da Hisbah: Yau za a ci gaba da shari’a

Hisbah za ta sake gurfanar da Murja Kunya a kotun Musulunci bayan an sako ta daga gidan yari sabanin umarnin alkali

A yau ne Kotun Musulunci da ke Kano za ta ci gaba da shari’ar jarumar TikTok Murja Ibrahim Kunya, wadda ake ce-ce-ku-ce bayan an sake ta daga gidan yarin da kotun ta ba da umarnin a tsare ta.

Za a sake gurfanar da Murja ne a shari’ar da Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ke zargin ta da laifin bata tarbiyya da koya wa kananan yara karuwanci da kuma tayar da hankalin al’umma.

Lamarin shari’ar Murja ya dauki sabon salo ne bayan an gano cewa an sake ta daga Gidan Yarin Kurmawa, inda aka tsare da ita, saɓanin umarnin kotun.

Kakakin hukumar gidan yarin, Musbahu Lawan Kofar Nassarawa, ya bayyana cewa kotun da ta ba da umarnin tsare Murja ce ta ba su umarnin sakin ’yar TikTok din daga baya, ta wata takarda da aka kawo musu dauke da sa hannun alkalin.

Sai da kuma kakakin kotunan Musulunci na Jihar Kano, Muzammil Ado, ya shaida wa ’yan jarida cewa babu wani lokaci da kotun ta ba da belin Murna, ballantana alkali ya ba da izinin sakin ta.

Wannan ka-ce-na-ce ya sa wasu yada rade-radin cewa Babban Kwamandan Hukumar Hisbah na jihar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ajiye kujerarsa, amma daga bisani hukumar ta ƙaryata.

Hukumar ta bayyana cewa aikinta shi ne na kama masu laifi da gurfanar da su, sauran kuma ba huruminta ba ne.

Wasu dai na zargin cewa da hannun gwamnati aka sake Murja, amma Gwamnatin Jihar Kano ta nesanta kanta da sakin ‘yar TikTok din daga gidan yarin.

Zuwa lokacin hada wannan labari dai ba mu samu jin ta bakin lauyan Murja ba game da wannan dambarwa.

Amma wani masanin shari’a a Kano, Barista Abba Hikima, ya bayyana cewa, matuƙar kotu ta ba da umarnin tsare wanda ake zargi ko ta dage shari’arsa, ba a sauya umarnin kotun sai idan wani abu na gaggawa ne ya taso.

A hakan ma, babu mai hurumin sakin sa ko sauya ranar ci gaban shari’ar sai alkakin da ya ba da wannan umarnin, ko idan kara aka daukaka.

Barista Abba Hikima ya ci gaba da cewa, idan kuma alkakin zai sauya umarnin da ya bayar na farko, dole sai an sake zaman kotu, an gabatar da lamarin a gaban lauyoyin bangarorin da ke shari’ar.

Kasa da mako guda ke nan da kotun da ke zamanata a Filin Hockey ta yanke wa saurayin Mutja da Hisbah ta kama su tare hukuncin daurin wata shida a gidan yari.

Za a sake gurfanar da Murna ne washegarin da wata kotun Musulunci a jihar ta yanke wa wata ’yar TikTok, Ramlat Muhammad hukuncin dauri a gidan yari kan laifin yada badala, fitsara da kuma yawon ta-zubar.

Tamkar ta fara shiga bakin duniya ne tun bayan wani bidiyon TikTok da ta yi, wanda a ciki take bayyana kanta a matsayin ’yar madigo.