✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yunkurin juyin mulkin: Mai kare lafiya ya harbe Hafsan sojin Ethiopia

Mai tsare lafiyar babban Hafsan sojin kasar Ethiopia, ya harbe uban gidan nasa, Janar Seare Mekonnen, tare da wani jami’in soja  yau. Su biyun sun…

Mai tsare lafiyar babban Hafsan sojin kasar Ethiopia, ya harbe uban gidan nasa, Janar Seare Mekonnen, tare da wani jami’in soja  yau.

Su biyun sun mutu ne a lokacin da suke kokarin dakile yunkurin juyin mulkin da aka so a yi a yankin Amhara da ke Arewacin kasar, in ji Firaiminista Abiy Ahmed.

Baya da mutanen biyu, an kuma kashe gwamnan yankin na Amhara, Ambachew Mekonnen tare da wani mai ba shi shawara.

Firaiminista Abbiy Ahmed ya shiga gidan talbijin din kasar, inda ya nemi ‘yan kasar da su hada kai su tunkari masu son wargaza kasar.

Daga Majiyar BBC