✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a ba duk kulob da ke gasar rukuni na kasa Naira miliyan 10

Kulob-kulob  da ke yin wasa a gasar rukuni-rukuni ta kasa da ake wa lakabi da Nigerian Premier League a makon gobe ne aka sa ran…

Kulob-kulob  da ke yin wasa a gasar rukuni-rukuni ta kasa da ake wa lakabi da Nigerian Premier League a makon gobe ne aka sa ran za su dara bayan da kamfanonin da ke daukar nauyin gasar suka ware wa kowane daga cikin kulob din da ke gasar Naira miliyan goma da rabi a matsayin kasonsu.
Idan za a iya tunawa, kimanin shekaru biyu ke nan da kulob din ba su samu ko sisin kwabo daga masu daukar nauyin gasar ba da hakan ya jefa da yawa daga cikinsu cikin matsala.
Labarin da muka samu ya nuna a makon gobe ne ake sa ran kowane daga cikin kulob din da ke wasa a gasar rukunin Premier ta Najeriya zai washe da Naira miliyan goma da rabi sai dai kudin bai hada da kason da kungiyoyin za su samu daga hukumomimn da ke da alhakin nuna gasar ta akwatin talabijin (Broadcasting right) ba.
Kamfanoni da ke daukar nauyin wasanni a kasashen ketare ba sabon abu ba ne sai dai a nan gida Najeriya abin ba haka yake ba, hakan take tilasta ’yan wasa su rika rububin barin kasar nan don samun kulob a kasashen ketare.
Rashin kudi ke sa kungiyoyin kwallon kafa da dama a Najeriya suke kasa biyan albashi da alawus din ’yan kwallo a tsawon lokaci.