✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a gina kasuwannin zamani 34 a Jihar Katsina

Gwamnatin jahar Katsina za ta gina kasuwannin zamani guda 34 a fadin jahar,inda za a gina guda daya a kowace karamar hukuma, a wuraren da…

Gwamnatin jahar Katsina za ta gina kasuwannin zamani guda 34 a fadin jahar,inda za a gina guda daya a kowace karamar hukuma, a wuraren da suka dace, ba lallai sai a hedkwatar karamar hukuma ba.
Tsohon kwamishinan Yada labarai da tarihi da al’adu na jahar ta Katsina kuma shugaban kwamitin riko na karamar hukumar  kafur Alhaji Nafi’u Lawal Kurungafa ne ya bayyana haka a makon da ya gabata a ofishinsa bayan ya kai ziyarar gani da wurin da ake ganin ya dace da a gina wannan kasuwar a yankinsa.
Shugaban ya ce,”wannan fili da ke kan wata mahada da ke tara jama’a a tsakanin Yari Bori da Dogon Marke a tsakankanin hanyoyin da suka taso daga karfi daKurungafa da Tsiga da’Yar kasuwa da kuma hanyar da ta taso daga Dogon Marke daYari Bori da kuma kafur”.
Alhaji Nafi’u ya da cewa, bayan duba filin tare da auna shi, za su mika wa kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jahar Katsina rahoto ya mika wa Gwamna don cigaba da abin da ya dace.
Har’ila yau, shugaban kwamitin riko na karamar hukumar ta kafur ya bayyana cewa,”kusan kashi 85 na mutanen yankin duk manoma ne, don haka wannan kasuwa za ta kara bunkasa harkokin kasuwanci, ba a karamar hukumar Kafur kawai ba, har ma a fadin jaha baki daya. “Wadannan kasuwannin za su bunkasa rayuwar matasa ta hanyar rage zaman kashe wando da kuma rage yawace-yawacen da suke yi a garuruwa ko kasashe da sunan neman kudi,wanda idan ba a yi sa’a ba sai su fada aikata mugayen dabi’u”.
 Shugaban sai  ya jinjina wa Gwamna Shema a kan wannan hangen nesan day a yi da kuma kokarin bunkasa harkokin kasuwancin da aka san jahar Katsina da su.
 “A nan, ina kira ga jama’a, musamman matasa da su rungumi sana’o’i da kasuwanci don su dogara da kansu, ba zama karkashin wani ko wadansu ba.”  Inji Alhaji Nafi’u Kurungafa.