✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Za mu takura wa masu fasa-kwauri wajen amfani da FTZ’ Mahmoud

Kwanturolan Hukumar Kwastam ta FOU, Shiyyar ‘A’ da ke Ikeja a Legas, Kwanturola Nuhu Isa Mahmoud, ya bayyana kudirin hukumar na magance shirin da masu…

Kwanturolan Hukumar Kwastam ta FOU, Shiyyar ‘A’ da ke Ikeja a Legas, Kwanturola Nuhu Isa Mahmoud, ya bayyana kudirin hukumar na magance shirin da masu fasa-kwauri ke niyyar yi na amfanin da shiyyoyin kasuwanci da ake kira FTZ wajen shigo da kayayyki ba bisa ka’ida ba.
Kwanturola Nuhu Mahmoud ya bayyana haka ne lokacin da suke tattaunawa da wakilinmu a ofishinsa da ke Ikeja, inda ya ce, wadannan kebabbun shiyyoyin na FTZ suna da muhimmanci ta fannin bunkasa tattalin arzikin kasa da samar da guraben ayyuka ga jama’a. Sai dai ya ce za su tabbatar sun fatattaki miyagun ’yan daga shiyyoyin kamar yadda shugabansu Alhaji Abdullahi Dikko Inde ya umarce su.
“Kwanturola Janar Abdullahi Dikko Inde, ya bayar da umarnin gaugawa na daukar matakin maganin irin wadannan ’yan kasuwa da suke kokarin mayar da kebabbun shiyyoyin zuwa dandalin fasa-kwauri,” inji shi.
Ya ce Babban abin da shiyyar FTZ, ya tanada shi ne, duk ’yan kasuwa na ciki da wajen Najeriya masu sha’awar kafa kamfanoni da masana’antu da za su rika odar kaya daga waje su yi amfani da na cikin gida wajen sarrafa su da darajarsu domin sayarwa ga kasashen duniya, kofa a bude take su shigo da na’urorin sarrafawa da sauran abubuwan bukatu ba tare da biya harajin ba. “Ka ga kenan, Najeriya za ta shiga cikin sahun kasashen duniya da suka ci gaba ta fannin hada-hadar kasuwancin irin kayan da suke sarrafawa suna sayarwa ga wasu kasashe, inda tattalin arzikinmu zai bunkasa a samar da guraben ayyuka ga dubban jama’a, amma wasu miyagun ’yan kasuwa suka bullo da dabarun ganin sun durkusar da wannan muhimmin shiri, kuma mun riga mun bullo da irin namu dabarun domin mu yi maganinsu,” inji Mahmoud.
Kwanturolan na FOU, ya ce duk da yake akwai garabasar shigowa da wasu kaya ta shiyyoyin FTZ ba tare da biyan haraji ba, ya ce “Akwai wasu kayan da dole ne sai an biya musu haraji, kuma irin wannan haraji ne wadannan ’yan kasuwa suke kin biya tare da bata mana suna wai muna so mu durkusar da arzikinsu. Sai su koma suna shigo da kaya ta haramtacciyar hanya maimakon halattacciyar hanyar da aka tanada musu.”
Ya ce “Muddin muna so harkokin kasuwanci su bunkasa a Najeriya lallai ne duk masu ruwa da tsaki su fito su ba da gudunmawasru tsakaninsu da Allah, wannan shi ne abin da Hukumar Kwastam take so a yi domin cimma buri. Muhimmin abu shi ne, duk kudaden da suka zama hakkin gwamnati ne, to, kwastam za su tabbatar cewa, sun karbe su. Na biyu ’yan kasuwa da kamfanoni da suka bi dokokin shigowa da kaya ta halattacciyar hanya, za mu tabbatar mun taimaka musu wajen ganin sun shigo da kayansu ba tare da wata matsala da za ta iya haifar da bacin ransu ko tayar da jijiyar wuya ba. Na uku shi ne tabbatar da ganin mun yi maganin masu shigowa da kaya ta haramtacciyar hanya.”
Kwanturola Mahmoud, ya ce, idan irin wadannan ’yan kasuwa ba sa so a rika bata musu lokaci wajen karbar kayan da suka yi oda daga kasashen duniya, “To, su ma su dauki matakan hanzarta sanar da mu cikin lokaci daga ranar da suka yi niyyar turo kayansu, su yi aiki kamar yadda doka ta tanada. Misali, idan ka sayi mota a kan Dala dubu 10 a wata kasar Turai, to, ka tabbatar mana da gaskiyar haka a Najeriya kada ka fadi karya wato kasa da yadda ka saya domin kauce wa biyan kudin haraji daidai da yadda ka sayo motar. Ka ga idan ka zo karbar kayanka daga hannunmu da sauran jami’an lura da shigo da kaya, ba za a samu matsala ba. Rashin fadin gaskiya daga ’yan kasuwa ne yake kawo dadewa ba su karbi kayansu ba tare da biyan kari kudin,” inji shi.
Ya ce idan kowa ya taka kyakkyawar rawa dangane da wannan al’amari, komai zai tafi daidai ba tare da wata matsala ko zargin juna ba.