✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben raba-gardama: Yadda APC da PDP suka sake sabon lale

Jam’iyyun APC da PDP da za su fafata a zaben raba-gardama na zaben gwamnoni a gobe sun sake sabon lale don ganin sun samu nasara…

Jam’iyyun APC da PDP da za su fafata a zaben raba-gardama na zaben gwamnoni a gobe sun sake sabon lale don ganin sun samu nasara a zaben.

Zaben na gobe  wanda ga alamu za a yi gumurzu a tsakanin jam’iyyun biyu shi ne na karshe a zaben gwamnonin jihohi da za a kammala a jihohi biyar da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta ce ba a kammala ba makonni biyu da suka gabata.

A makon jiya Hukumar INEC ta ce za a gudanar da zaben ne a jihohi shida, kafin ta cire Jihar Bauchi daga baya.

Jihohin da za a yi gumurzun karshe a goben sun hada da Kano da Sakkwato da Filato da Adamawa da Benuwai, inda kowace jam’iyya da dan takararta suka ja daga don kaiwa ga nasara.

A Jihar Kano Gwamna Abdullahi Ganduje yana gudanar da ayyukan raya kasa a wasu wuraren da za a sake gudanar da zaben musamman a mazabar Gama, inda gwamnatin ta shimfida wa al’ummar yankin makeken titi tare da gina musu rijiyoyin burtsatse 11 da aikin sanya tayil a Asibitin Isa Kaita da kuma aikin ginin masallaci. Kuma an gudanar da aiki ga masu ciwon ido kyauta a yankin.

Sannan Uwargidan Gwamnan, Hajiya Hafsatu Ganduje ta yi bikin raba wa mata masu juna biyu kayan haihuwa da kuma jari ga wadansu matan yankin.

A jawabinsa ga manema labarai Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce ayyukan da gwamnatinsa ke yi a Unguwar Gama ayyuka ne da dama suke kan tsari kuma aka gudanar da su don Allah.

“Shi aikin alheri ba a makara da yin sa, dukan ayyukan da ake yi a yanzu ayyuka ne da suke a kan hanya sai a wannan lokaci ne dai aka samu damar gudanar da su,” inji shi.

Ana dai zargin ’yan siyasa da sayen kuri’a daga jama’a a yankunan da za a sake zaben na Kano. A wani rahoto da Aminiya ta yi a baya an ji yadda ’yan sanda a jihar suka kama mutum shida kan zargin sayen kuri’u, kuma an kama mutum hudu daga cikinsu ne a Unguwar Gama, biyu a Karamar Hukumar Dala.

Wadanda aka kama sun shaida wa Aminiya cewa wadansu jiga-jigan Jam’iyyar APC ne suka sanya su wannan aiki na sayen kuri’u daga jama’a.

Jam’iyyar APC ta kuma zargi Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Muhammad Wakili da kokarin taimaka wa Jam’iyyar PDP wajen yin magudi a zaben raba-gardamar na gobe Asabar.

Wata takarda dauke da sa hannun Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar ta Kasa, Mista Lanre Issa-Onilu, APC ta ce, Kwamishinan ya ba magoya bayan Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ’yan sandan kariya yayin da ya janye wa kwamishinonin jihar nasu ’yan sandan.

“A bayyane yake yadda Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano ya taimaka wa Jam’iyyar PDP domin ta yi magudi a cikin birnin Kano a zaben da za a yi a gobe Asabar. Yanzu haka Kwamishinan ya ba magoya bayan Kwankwaso ’yan sandan kariya yayin da ya janye ’yan sandan da ke ba kwamishinonnin jihar kariya,” inji sanarwar.

Jam’iyyar APC ta ce Jihar Kano cibiya ce ta Jam’iyyar APC, don haka PDP ba ta da mazauni a jihar, ta ce tana da tabbacin samun nasarar zaben da za a gudanar.

Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa Sanata Bola Tinubu a shekaranjiya Laraba ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa ya je Kano kan zaben raba-gardamar.

Tinubu ya fadi a wata sanarwa dauke da sanya hannun Kakakinsa Tunde Rahman, cewa hotonsa da ake nunawa a shafukan sada zumunta shi da Gwamna Ganduje an dauke shi ne a bara lokacin da Gwamnan ya ziyarci Legas. Ya ce irin wannan jita-jita za ta iya yin illa ga dimokuradiyya a daidai lokacin da ake kokarin dasa akidar ci gaba kamar yadda Kano ta yi fice a kai.

A bangare Jam’iyyar PDP kuwa ta ce ta tashi haikan ne wajen yakin neman zabe ta bin wuraren da zaben raba-gardama ya shafa a jihar don tallata dan takararta Injiniya Abba Kabir Yusuf.

Kakakin dan takarar, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya shaida wa Aminiya cewa duk da matakan da Jam’iyyar APC ke dauka na neman kuri’a ta kowane hali, jam’iyyarsu na da tabbacin lashe zaben. “Muna yakin zabe gida-gida. A yanzu haka jama’armu da ke yankunan da za a sake zaben suna can suna gudanar da yakin zabe, Mu kuma a nan mun je Karamar Hukumar Dala da ita kanta mazabar Gama,” inji shi.

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta bakin Kakakinta DSP Haruna Abdulahi Kiyawa ta tabbatar wa al’ummar jihar samun tsaro a yayin zaben raba-gardamar.

DSP Kiyawa ya ce za su samu taimakon ’yan sanda daga jihohin da ke makwabtaka da jihar don sanya ido a kan zaben, kuma ya ce wKwamishina Wakili yana ganawa da masu ruwa-da- tsaki a wuraren da za a gudanar da zaben don ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Rundunar ta yi kira ga jama’ar su ba ’yan sandan hadin kai a lokaci da kuma bayan gudanar da zaben.

A Jihar Sakkwato zaben na gobe tsakanin Gwamna Aminu Tambuwal na PDP wanda ya ba dan takarar APC, Ahmad Aliyu ratar kuri’a shi 3,413, masu lura da siyasar jihar suna ganin APC tana iya kwace kujerar ganin kuri’un kananan hukumomin Kebbe mai dubu 20,150 da Gada mai dubu 13 da 314, Jam’iyyar APC ke da karfi a cikinsu. Sai dai kuma Gwamna Tambuwal da mukarabansa sun ja daga don ganin sun ci gaba da rike nasarar da suka samu tun farko.

Abubakar Balarabe Dandinmahe dan Jam’iyyar PDP ya shaida wa wakilinmu cewa “Wannan zabe da za a yi tarihi ne zai maimaita kansa don mu ne ke da nasara. Nasararmu ta zo wa magoya bayan Jam’iyyar APC da mamaki, sun dauka za su lashe zaben cikin sauki don suna da sanatoci 3 da ’yan Majalisar Wakilai tara. Yanzu sun gane Sakkwato ta Sakkwatawa ce ba wani mai ita, kuma sun aminta Tambuwal za su bai wa kuri’unsu a karo na biyu, duk mai jayayya ya bari nasarar da PDP ta samu za ta ci gaba da tabbata cikin zaman lafiya”

Umar Dan Barade na APC ya ce “Yakininmu na cin zaben Gwamna a jihar ya yi mana illa kadan saboda muka sakankance muka manta batun karfin da Gwamna ke da shi a jiha, saboda ganin nasarar da muka samu a zaben farko. Amma yanzu tsiminmu ya motsa, mun fi su magoya baya a jiha, kudin da suka yi amfani da su da wuya su yi aiki a yanzu. Za mu kasa mu tsare mu raka, fatata mu san bambancin siyasa ba abu ne da zai sa mu riki junanmu da gaba da kiyayya ba, kowa ya yi ra’ayinsa amma a gimama juna, cin zarafin juna ba na Sakkwatawa ba ne.”

Shugaban Jam’iyyar PDP na Sakkwato ta Tsakiya, Alhaji Muhammad Dangwaggo ya ce sun gamsu da alkawarin da Kwamishinan Zabe na Jihar ya dauka na rike amana da rashin nuna karkata. “Allah Ya riga ya zabi wanda zai ci zaben mun dauki matakin hana tarzoma a lokacin zabe,” inji shi.

Sakataren Jam’iyyar APC na Jihar, Alhaji Abubakar Muhammad ya ce kan zabe na gobe jam’iyyarsu ta yi kira ga magoya bayanta su zauna lafiya. “Tashin hankali ne ya kawo rashin kammala zaben, jiki magayi ga jam’iyyu, ya kamata mu san Allah Ya gama komai Ya hukunta wanda zai zama Gwamna, ba sai mun yi fada da juna ba. Su kuma hukumar zabe da jami’an tsaro su yi adalci a zaben, su kare masu jefa kuri’a muna nanata a zauna lafiya a jiharmu da ikon Allah mu ke da nasara,” inji shi.

Kwamishinan Zabe na Jihar Sakkwato Muhammad Sadik Abubakar ya ce rumfunan zabe 135 ne za a yi zaben sabanin yadda aka fadi da farko, kuma shi ne jami’in karbar sakamakon zabe na Karamar Hukumar Kebbe wadda aka samu hatsaniya sosai a baya fiye da sauran wurare.

Kwamishinan ya ce bai kamata ’yan siyasa a lokacin taro su nuna ba komai a tsakaninsu ba sai alheri, amma in sun koma wajen yakin zabe su zama kamar makiya juna.

“An sare yatsun hannun ma’aikacinmu yanzu haka ba ya iya komai da hannunsa, daya an bata kayan gwamnati gaba daya a gaban jami’an tsaro ’yan siyasa ne suka sanya a yi haka, sun sanya yara matasa su yi fada don hana zabe ya gudana hakan bai dace ba ku yi wa magoya bayanku magana,” inji shi.

A Jihar Bauchi kuwa shari’u ne suka dabaibaye batun zaben na raba-gardama. Da farko Jam’iyyar PDP ce ta je kotu tana neman a bayyana dan takararta Sanata Bala Mohammed a matsayin wanda ya lashe zaben, bayan Hukumar INEC ta bayyana zaben Gwamnan Jihar da wanda bai kammala ba. Daga baya wani kwamitin Hukumar INEC ya umarci a ci gaba da amsar sakamakon zaben Karamar Hukumar Tafawa Balewa, lamarin da ya sanya Gwamna Mohammed Abubakar da Jam’iyyar APC suka je kotu suna kalubalantar matakin.

Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta dakatar da tattara sakamakon zaben zuwa lokacin da za ta saurari karar da Jam’iyyar PC da Gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar suka shigar a gabanta.

Ita ma Jam’iyyar PDM ta kai karar Hukumar INEC kotu tana neman hukumar ta bayyana dan takarar jam’iyyar Alhaji Ahmed Iliyasu cewa shi ya lashe zaben Gwamnan Jihar ko ta soke zaben, saboda hukumar ba ta sanya alamar jam’iyyar a takardar kada kuri’a ba a zaben wanda haka ya sa magoya bayanta suka gaza yin zabe.

Lauyan Jam’iyyar Barista Auwalu Idris Kwami ne ya sanar da haka bayan sun shigar da kara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Bauchi, inda ya ce Jam’iyyar PDM ta cika dukan ka’idoji da dokoki wajen tsayar da ’yan takara, amma INEC ta gaza sanya tambarin jam’iyyar a takardar zaben da aka gudanar a ranar Asabar 9 ga Maris.

Sauran jihohin da za a fafata su ne Filato inda Gwamna Lalong na APC ya ba Jerry Useni na PDP tazarar kuri’a fiye da dubu 44, kuma za su fafata ne a kan kuri’a dubu 49.   A Jihar Adamawa ma za a fafata ne a tsakanin Gwamna Bindow na APC da ke biye da dan takarar PDP Ahmadu Fintiri a yawan kuri’u. Sai Benuwai a tsakanin Gwamna Ortum na PDP wanda ke gaban Emmanuel Jime na APC a yawan kuri’u, kamar yadda muka ruwaito a makon jiya.

Tuni Kwamitin Zaman Lafiya na Kasa a karkashin Janar Abdulsalami Abubakar ya zauna da masu ruwa-da-tsaki don ganin an gudanar da zabenraba-gardamar lami lafiya.

Daya daga cikin wakilan kwamitin Bishop Mathew Hassan Kuka ya fadi a wurin wani taron masu ruwa-da-tsaki a Sakkwato cewa dukan’yan takarar ’yan asalin Jihar Sakkwato ne kuma duk yaron da ya samu rauni dansu ne komai bambancin jam’iyya, inda ya ce halin da wadansu ’yan siyasa ke nunawa abin takaici ne.

Bishop Kukah wanda ya ce yana wakiltar Janar Abdulsalami Abubakar ne ya jawo hankalin masu ruwa-da-tsaki a zaben su guji tashin hankali su zauna lafiya da mutunta juna duk wanda ya samu nasara a goya masa baya.

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce zaman lafiya ne ginshikin komai ba abin da za a samu in ba zaman lafiya don haka jama’a su yi zabe cikin lumana.

Sarkin Musulmin wanda Wazirin Sakkwato Farfesa Wali Junaid ya wakilta ya ce, “Mu daina mantawa mu Musulmi ne komai namu akwai tsarin da addini ya aminta mu yi.”