✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zafin nakuda ya sa wata ta farke cikinta da reza

Wata mata mai suna Hassana Maikudi da ke kauyen Bedi a Karamar Hukumar Ganjuwa da ke Jihar Bauchi ta sa reza ta farke cikinta saboda…

Wata mata mai suna Hassana Maikudi da ke kauyen Bedi a Karamar Hukumar Ganjuwa da ke Jihar Bauchi ta sa reza ta farke cikinta saboda zafin nakuda.

Aminiya ta samu labarin cewa matar ta farke cikinta ne tun daga kirjinta har zuwa tumbinta.

Majiyarmu ta ce matar ta fara nakuda ne da misalin karfe 8:00 na dare sai mijinta ya fita shaida wa kanwarsa don ta zo ta taimaka mata, amma dawowarsa gida shi da kanwar ke da wuya, sai suka same ta cikin mawuyacin hali, sakamakon daukar sabuwar reza da ta yi ta farke cikinta, tun daga kahon zuciyarta har k an tumbinta, watakila da nufin ciro abin da ke cikin nata, al’amarin da ya firgita jama’ar kauyen.

Matar wacce shekatun ta goma tare da mijinta ta haifi ’ya’ya bakwai koda yake a baya ta taba yin aure inda ta haifi da daya.

Sai dai mutanen kauyen suna mata kallon mace da take da tabin hankali.

Mijin matar Malam Muhammadu Maikudi ya bayyana wa Aminiya cewa “Abin da ya faru da ita ranar Lahadin da ta gataba shi ne ya dawo daga kasuwa lokacin an gama abinci sai ya ce ta wajensu yau kasuwa ba ta dadi ba, sai yara suka ce ya ba su abin kayan maraba da dawowa daga kasuwa. Ya ce bayan gama abinci sai Sarkin Noma ya zo suka shiga daki suna tadi sai yalinsa ta kira shi, da yaje sai ta ce ya je ya kira mata kanwarsa don ta ji cikinta yana taba ta.

Maikudi ya ce “Na shiga cikn gida na kira Sarkin Noma na ce masa ga abin da yake faruwa ya zo ya raka ni, mun kama hanya sai na ce ina ganin kamar nakuda ne bari in kira Amaza. Na ce bari in ba ta shawara na ce wance ga yadda za a yi. Amma ta ce ni dai ka je ka kira ta, na dawo na ce da Sarkin Noma ga shawarar da na ba ta amma ta ce ba haka ba. Sai ya ce ka zo mu je mu dawo. Sai na ce ina kaulani ya ce za mu je mu dawo, muka je na samu kanwata ta yi lalle a kafa daya saura daya na ce ga abin da ake ciki. Sai ta tashi a firgice muka taho, to da yake matata ba ta da hankali sosai, kawai sai ta dauki reza ta danna a kasar marufin kirjinta data danna sai ya yi kasa ta cire. Da muka iso sai muka shige ashe lokacin ita iyalina tana cewa ka zo, ka zo da kanwata ta shiga dakin sai ta ce mata cikina ya fashe. Sai kanwata ta duba ta ce “Innalillahi wa inna ilaihi rajiu’n, kin kashe kanki, me ya sa kika yi haka?”

Ya ce “Muna fitowa daga daki sai kanwata ta ce Yaya aiki ya baci na yi istirja’i, na shige dakin na ga wurin da ta farke da rezar fari sal, jini bai fara fitowa ba, na rikice na buga nan na buga can ga fitila a daki amma duhu nake gani. Nan na fada wa Sarkin Noma muka fita neman mota ba mu samu ba sai muka kira Sarki, da ya zo ya nemo mota ana cikin tafiya aka ce ai ta rasu.”

Ya ce “Lokacin da kanwata ta zo kawai sai ta dauki rezar za ta boye, sai kanwata ta ce me za ki yi bayan kin kashe kanki? Ta haifi ’ya’ya bakwai tare da ni kuma ba ta taba aikata wani abin tashin hankali ba. A bazawara na aure ta ta haihu a gidan da ta fara aure kuma abin mamaki a ranar ita ta yi abinci ta ba da yara ta ci nata.”

Sarkin kauyen Malam Muhammadu Idris ya ce abin ya faru ne ranar Lahadin da ta gabata ya tafi zai karbo wasu magunguna saboda wani dansa bai da lafiya, sai wani yaro ya zo ya same su da Alhaji Danlami ya ce wan inji Isiyaka in kira lambarsa akwai mata tana maganar haihuwa “Sai na dauka ko irin zubar jinin nan ne da ke samun mata masu juna biyu, sai na kira lambar Isiyakan da ya amsa sai ya ce min Sarki matar Malam makwabcinka ne ba ta da lafiya nakuda ta taso mata. Sai na ce Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un na garzaya gida, ina isowa na same su sun yi cirko-cirko, na ce me yake faruwa suka ce marigayiyar ce nakuda ta taso mata ta dauki sabuwar reza ta farke cikin.”

Ya ce “Sai na ce mu yi maza mu kai ta asibiti na sa aka fito da babur aka je aka samu Ciroma ya zo da mota muka yi kokarin kai ta asibiti, na nemi kudi na rike don mu ceto rayuwarta saboda tana mawuywacin hali, a baya mun san ga yadda yanayin hankalinta yake muka yi kokarin isa asibiti Allah da ikonSa ba mu karasa asibiti ba ta rasu sai muka dawo.”

Sarkin ya ce sai ya ba da umarni a je a sanar da hukuma ta san abin da ya faru kuma a yi musu bayanin yanayin yadda matar take don a nan kowa ya san halin da take ciki.

Sarki Muhammadu ya ce “Lokacin da aka kira ni na same ta da ranta tana tsaye ana yi mata magana me ya sa kika aikata haka? Sai ta yi maka ido ta yi maka shiru ba ta cewa komai kuma ga rezar da ta tsaga cikinta a gefe, sai na ce ba amfani a yi ta maganganu a yi kokari a kama wurin a daure ko jinin zai daina zuba, amma batun rauni hakika yanayin raunin tsawonsa bai wuce daga cikin tafin hannu zuwa karshen yatsa ba, inda ta farke da rezar kuma jini ya zuba sosai har ya kai kana iya hangen cikin tumbinta don ta gama kure fatar duka.”

Sarkin ya ce saboda ba su da wani asibiti a kusa sun yi niyyar kai ta Babban Asibitin Bauchi ne lokacin da suka dauke ta sai Allah Ya dauki rayuwarta.

Ya ce bayan sun shaida wa hukuma sun zo sun dauki hotunanta, suka kuma nemi karin bayani kan yanayin matar inda aka shaida musu cewa tana da ’yan matsalar tabin hankali.

Ya ce da wuya ka ga marigayiyar ta shiga wajen wani ko wani abu ya faru, ba ta magana da kowa tana zaune ne kawai abinta, in mutum ne ya shiga gidan da take ya yi mata magana za ta amsa in bai mata magana ba tana shiru ta zuba masa ido kawai.

Sarkin ya ce rasuwar mata ta sa jikin mutane ya yi sanyi kuma lamarin ya ba su tsoro sosai, ya ce du wanda ya ga abin da ya faru da dan Adam irin wannan dole ne ya tausaya masa, kuma dole hankalinsa ya tashi ya shiga dimuwa. “Abin tausayi ne kuma abin al’ajabi ne sai dai tawakkali tunda duk halittar da ka ga Allah Ya yi kowanne da yadda zai shiryo shi da irin abin da Allah Ya nufa zai yi. Muna rokon Allah Ya kare faruwar irin haka nan gaba, ita kuma muna yi mata addu’ar Allah Ya gafarta mata,” inji shi..

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi, DSP Kamal Datti Abubakar ya ce zai tuntubi manema labarai idan ya kammala wani aiki, sai dai har zuwa turo wannan rahoto bai tuntuba ba.