✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan kalubalanci hukuncin kotu kan nasarar Lalong – Useni

Dan Takarar Gwamnan Jihar Filato a Jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, Sanata Jeremiah Useni ya ce zai kalubalanci hukuncin da kotun sauraren kararrakin…

Dan Takarar Gwamnan Jihar Filato a Jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, Sanata Jeremiah Useni ya ce zai kalubalanci hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke na ba wa Gwamna Simon Lalong nasara.

Mataimaki na mussamman kan harkokin wasta labarai ga Sanata Useni, Yijap Abraham ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Jos. Ya ce tuni lauyoyinsa a karkashin jagorancin Mike Ozekhome (SAN) da Edward Pwajok (SAN) sun ba da sanarwar daukaka karar.

Sanata Useni da Jam’iyyar PDP sun dage cewa Gwamna Simon Lalong bai cancanci zama Gwamna ba, domin ya ba wa Hukumar Zabe bayanai na karya, “Hakazalika batun da kotun zaben ba ta tabo ba, shi ne mutum na biyu cikin wadanda ake karar bai dace ya  fito takarar Gwamna ba, amma sai kotun ta yi gaban kanta ta juya al’amura ba yadda suke ba, wanda ya saba tsarin shari’a, don haka ne za mu daukaka kara zuwa kotu ta gaba,” inji Useni.