Search
Subscribe
Boko Haram ta saki bidiyon mutanen da ta kama suna neman dauki

Shugaban Bangaren Boko Haram Abubakar Shekau

Boko Haram ta saki bidiyon mutanen da ta kama suna neman dauki

Ma’aikatan jinkai da kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su a farkon watan Yuni sun roki Gwamantin Najeriya da kungiyoyin da suke wa aiki su ceci rayuwarsu.

Kungiyar Boko Haram ta fitar da wani bidiyo da ke nuna ma’aikatan su hudu suna rokon Gwamantin Tarayya ta yi abin da ya kamata domin Boko Hram ta sako su.

Ma’aikatan sun hada da na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jiha da kuma ‘yan kungiyar Agaji ta Action Against Hunger, Rich International, International Rescue Committee da kuma mai aikin tsaro.

Rahotannin baya sun bayyana yadda mayakan kungiyar suka yi garkuwa da wasu ma’aikatan agaji a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Monguno a jihar Borno.

“Sunana Abdulrahman Babagana; ni ne Manajan Sansani na SEMA a Monguno. Sun kama ni bayan na bar Monguno a hanyata ta zuwa Maiduguri, kuma yanzu muna hannunsu a sansaninsu.

“Ina rokon gwamnati ta kawo mana dauki. A ranar 1 ga watan Yuni suka kama mu. Yanzu ina magana ne a ranar 21 ga watan. Don Allah ku cece mu”, inji Abdulrahman Dungus, ma’aikacin Rich International.

Wani abokin akinsa ya ce a hanyarsa ta komawa Monguno inda yake zama ne aka kama su a ranar 8 ga watan Yuni.

“Ina rokon kungiyar da nake wa aiki ta yi dukkan mai yiwuwa domin kubutar da ni daga hannunsu”, inji shi.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin