✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zanga-zangar #EndSARS ta rikide zuwa tashin hankali a Kano

An kashe mutane an farfasa shaguna tare da satar dukiyoyi a unguwar Sabon Gari

An kashe mutum hudu tare da jikkata wasu da dama a yankin Sabon Gari da ke Karamar Hukumar Fagge ta jihar Kano bayan a yayin da ake ci gaba da zanga-zangar #EndSARS.

A safiyar Talata wasu gungun matasa suka far wa masu zanga-zangar wadanda suka cika wandonsa da iska domin tsira.

Daga bisani zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali, inda matasa da dama daga unguwar Brigade a Karamar Hukumar Nassarawa da ke makwabtaka da yankin Sabon Gari suka farmaki masu zanga-zangar.

Sai dai rahotannin na bayyana cewa bata-gari ne suka yi amfani da zanga-zangar wajen ta da hankalin al’ummar yankin Sabon Gari da  kuma wani bangare na unguwar Brigade.

Bata-garin sun farfasa gilasan motoci tare da kona wasu motocin da aka ajiye a bakin hanya.

Har ila yau, bata garin sun fasa babban shagon sayar da kayayyaki na ‘Galaxy Mall’ da ke kan titin Igbo a Sabon Gari, inda suka sace kayyaki da dama.

Sun kuma fasa shagon saida abinci na ‘Chicken Republic’ da ke kan titin Aiport wanda shi ma suka yi barna a cikinsa.

Daga bisani jami’an ‘yan sanda sun kai dauki ga yankin na Sabon Gari domin kwantar da wutar rikicin.